Kasar Amurka ta bayyana aniyarta na tabbatar da an yi zaben gaskiya a Bayelsa

Kasar Amurka ta bayyana aniyarta na tabbatar da an yi zaben gaskiya a Bayelsa

Gwamnatin kasar Amurka ta dauki alwashin daukan tsaurara matakai a kan duk wanda aka kama da hannu wajen aikata magudin zabe tare da tayar da zauni tsaye a yayin zaben gwamnanjahar Bayelsa dake karatowa.

Shugaban ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, Claire Pierangelo ne ta bayyana yayin da take ganawa da manema labaru a jahar Legas a ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamba, inda tace zasu sanya idanu sau da kafa don tabbatar an yi zaben gaskiya.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kashe magajin garin wani kauye, sun sanya ma jama’a haraji

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanya ranar 16 ga watan Nuwamba domin gudanar da zaben gwamnan jahar Bayelsa da na Kogi, haka zalika za ta gudanar da zaben Sanatan mazabar Kogi ta yamma, duk a ranar.

“A matsayinmu na kawar Najeriya da jama’anta, zamu duba yiwuwar dabbaka wasu matakan ladabtarwa a kan masu karya dokokin zabe, za mu shiga filin zabe a matsayinmu na masu sa ido don gane ma idanunmu yadda komai zai kasance.

“Ina sane da cewa kasashe da dama da kuma kungiyoyi masu zaman kansu zasu sanya idanu a zaben Bayelsa, don haka zamu yi aiki tare dasu don tabbatar da an gudanar da ingantaccen zabe da babu cuta babu cutarwa a cikinsa.” Inji ta.

Haka zalika Uwargida Claire ta yi kira ga hukumar INEC da ta kasance mai adalci ba tare da daukan bangare ba, kuma ta nemi INEC ta jajirce kada ta yadda wani daga waje ya nemi ya juyata.

Jakadiyar ba ta tsaya a nan ba, har sai da ta yi jan hankali tare da gargadi ga hukumomin tsaro, wanda ta nemi su kasance masu nuna kwarewa wajen tabbatar da tsaro a zaben, domin mutanen Bayelsa su kada kuri’unsu cikin kwanciyar hankali.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel