Jami’an Kwastam sun dakile haramtattun kayan abinci a Garin Legas

Jami’an Kwastam sun dakile haramtattun kayan abinci a Garin Legas

Yayin da jami’an kwastam masu maganin fasa kauri a kasar nan su ka haramta shigowa da kaya ta iyakar kasa, an tare yunkurin da wasu su ka yi na shigo da kayan abinci ta tashar sama.

Jami’an hukumar kwastam sun tare haramtattun kayan abinci na Naira miliyan 68.9 a babban filin jirgin saman kasar na Murtala Muhammed da ke Garin Legas a cikin farkon makon nan.

A wani jawabi da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa an samu wannan kaya ne a tashar jirgin sama bayan rufe iyakokin kasa. Adewale Adeniyi da Lena Oyama su ne su ka bayyana wannan jiya.

Jami’an biyu ne su ka wakilci bangarorin hukumar wajen zantawar da aka yi da ‘yan jarida, su na cewa wannan ne karon farko da aka yi kokarin shigo da haramtattun kaya ta tashar jirgin sama.

KU KARANTA: Saboda na rabu da Mijina, IGP aka daure Mahaifi na - ASD Jr.

“A daren 10 ga Watan Nuwamba, bayan sauke kayan taragon jirgin kamfanin South African Airways mai kirar 5A060 da ya taso daga Garin Johannesburg, Ma’aikatunmu sun tare wasu kaya da aka bincika. An tare kwalaye 40 sannan kuma kwalaye 104 da aka yi watsi da su a jirgi.”

Jawabin hukumar ta NSC ya kara da cewa: “Ma’aikata sun nemi su duba kayan kafin su mikasu. Duk da takardu sun nuna cewa kayan ganye ne aka dauki, amma daga baya mu ka gane cewa sankararrun kayan abinci. A cikin kwalayen 40 akwai naman babbar dabba, naman alade da kifi.

Jami’an sun kuma sanar da Duniya cewa sun samu wasu kwalaye dauke naman alade, naman kaza, da talo-talo da aka yi watsi da su a filin sauka da tashin jirgin bayan an biya masu kudi.

Masu wannan kaya sun yi wannan dabara ne domin shigo da abubuwan da aka haramta cikin kasar ta bayan fage. An biya wa wadannan kaya kudin shiga na Naira miliyan 68.9, inji jami'an.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel