Yanzu-yanzu: DSS ta bayyana dalilin da yasa ba ta saki Sowore ba

Yanzu-yanzu: DSS ta bayyana dalilin da yasa ba ta saki Sowore ba

Hukumar Jami'an tsaro na farin kaya (DSS) ta yi ikirarin cewa a shirye ta ke ta saki dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC a zaben 2019 kuma mawallafin Sahara Reporters, Omoyele Sowore sai dai wadanda suka zo karbarsa ne ba su cancanta ba.

Hukumar ta yi wannan jawabin ne ta bakin mai magana da yawunta, Peter Afunaya ya fadi a ranar Laraba kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Afunaya ya kuma karyata cewa jami'an hukumar sun bude wa masu zanga-zanga wuta a ranar Talata.

Ya ce, "Kawo yanzu wadanda suka so karbarsa ba su da wata alaka da batun saboda haka ba su da ikon karbarsa yayin da wasu kuma suna can gefe suna ta amfani da lamarin don cimma manufarsu ta siyasa.

"A kwanakin baya-bayan nan, mutane da kungiyoyi daban-daban suna ta yadda kalamai na batanci da barazana don bata sunan hukumar.

DUBA WANNAN: Babbar mota ta murkushe mutum 20 sakamakon bin ta da 'yan sanda suke

"Ba za mu kula duk wasu masu neman tayar da fitina ba. Ina kira ga kafafen yadda labarai da 'yan jaridu su rika yin adalci tare da fadin gaskiya yayin yin aikinsu.

"Abinda ya dace shine wadanda suka tsaya masa yayin karbar beli su zo su karbe shi amma ba wasu daban ba.

"Hukumar DSS tana son ta tabbatar wa al'umma cewa jami'an ta ba su budewa masu zanga-zanga da suka zo harabar hukumar wuta ba a ranar 12 ga watan Nuwamban 2019.

"Kamar yadda ya ke a tsarin aiki a duk duniya, jami'an hukumar sun kare hukumar yayin da wasu kungiyoyin mutane su kayi yunkurin shiga cikin inda Sowore ya ke ajiye da niyyar fitar da shi da karfi da yaji.

"Duk da irin wannan yunkurin na tayar da hankali, jami'an DSS ba su harbi masu zanga-zangar ba. Babu yadda za ayi suyi hakan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel