Majalisa: Zafi ya sa Sanatocin Najeriya sun gaza aiki – Ahmad Lawan

Majalisa: Zafi ya sa Sanatocin Najeriya sun gaza aiki – Ahmad Lawan

Mun samu labari a yau Laraba cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Ibrahim Lawan, ya fito ya koka a kan cewa akwai matsanancin zafi a cikin ginin majalisar tarayyar.

Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya yi wannan kuka ne a Ranar Talata, 12 ga Watan Nuwamban 2019. Shugaban Sanatocin kasar ya ke cewa zafin da su ke fuskanta ya hanu su yin aikinsu.

A cewar Ahmad Lawan, zafin da ake fama da shi a cikin harabar majalisar kasar ya hana ‘yan majalisar dattawan gudanar da nauyin da aka damka masu, tuni dai ya dauki mataki a kai.

Ahmad Lawan ya umarci Akawun majalisar dattawan watau Mista Nelson Aywor ya yi maza ya tabbatar duk wasu na’urorin da ke sa sanyi da ke majalisar su na aiki kamar yadda ya kamata.

KU KARANTA: Sanatoci sun tona asirin barnar Jami’an hukumar NNPC

An dade ana yawan yin kuka game da yadda aka tsara wasu gine-ginen gwamnati a Najeriya. Wasu jami’an kasar kan karkatar da kudin da ake warewa domin kula da wurare cikin aljihunsu.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da majalisar tarayya ta ke fadi-tashi na ganin ta kammala aikin kasafin kudin shekara mai zuwa. Majalisar ta na so ta karkare aikin ne a cikin Watan nan.

Idan ba ku manta ba kwanakin baya aka samu labari cewa wata badakala ta barke a majalisar inda ake zargin Ahmad Lawan da tattare wasu kason aiki da aka rabawa 'Yan majalisar kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Online view pixel