Matar da aka garkame na shekaru biyu ta samu 'yanci

Matar da aka garkame na shekaru biyu ta samu 'yanci

Wata kungiyar taimakon kai da kai mai suna Arida Relief Foundation da hukumar 'yan sanda sun yi nasarar bankado wata mata mai suna Hassana Sale , wacce aka garkame a wani daki mai duhu na shekaru biyu. 'Yan uwan Hassana sun yi hakan ne don gudun kada ta koma gidan mijinta da suke zargin yana cutar da ita.

Kungiyar taimakon kai da kan da hukumar 'yan sanda sun tarar da mahaifiyar 'ya'ya hudun a cikin mawuyacin hali a ranar Litinin a yankin Rigasa na jihar Kaduna.

Kamar yadda shugabar kungiyar, Hajiya Rabi Salisu ta bayyana, babban yayan Hassana Sale ne ya tauye mata 'yancinta. Malam Lawal sale yayi hakan ne sakamakon niyyarta na komawa gidan aurenta.

Salisu ta bayyana cewa, Hassana ta fada cikin damuwa ne tun bayan da mijinta ya saketa. Saboda soyayyar 'ya'yanta ne take zuwa ganinsu lokaci zuwa lokaci.

DUBA WANNAN: IGP ya daure mahaifina saboda aurena da abokinsa ya mutu - Wata mata ta koka

"Tana ziyartar 'ya'yanta kullum. A don haka ne yayanta da wasu 'yan uwanta suka yanke shawarar garkameta a daki mai duhu na shekaru biyu ta yadda ba zata koma ga tsohon mijin nata ba," ta sanar da kamfanin dillancin labarai a ranar Talata a Kaduna.

"Mun kai ta asibiti kuma idan ta sammu daidaituwa zamu mika ta ga ma'aikatar walwala da jin dadin 'yan kasa don duba lamarinta."

Tuni jami'an 'yan sanda suka cafke yayan nata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel