'APC' ta dakatar da Gwamna Obaseki da mataimakinsa a kan zargin za su koma PDP

'APC' ta dakatar da Gwamna Obaseki da mataimakinsa a kan zargin za su koma PDP

Wani sashin jam'iyyar APC na jihar Edo mai suna Edo People Movement, a ranar Laraba ya sanar da dakatar da Gwamna Godwin Obaseki da mataimakinsa, Philip Shaibu tare da sakataren gwamnatin jihar, Ogie Osarodion.

Yayin sanar da dakatarwar a wani taronsu da kuma tattaunawa da manema labarai wanda aka yi a gidan Janar Charles Airhiavbere a Benin, Patrick Ikahriale wanda ya karanta jawabin a madadin EPM ya ce, "Kamar yadda muka samu labari daga manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP, gwamna Obaseki, mataimakinsa, Philip Shuaibu, Anslem Ojezua da sakataren gwamnatin jihar, Osarodion Ogie sun kammala shirye-shiryen barin APC zuwa PDP don tsayawa takara,"

DUBA WANNAN: Babbar mota ta murkushe mutum 20 sakamakon bin ta da 'yan sanda suke

A cewarsa, "A matsayinmu na sahihan masu ruwa da tsaki na APC a jihar Edo, mun kalubalanci hakan. Muna so mu sanar akan lokaci, kwamitin aiki na kasa na jam'iyyar APC sai fara tantance dan takarar gwamnan jihar. Zamu kiyaye wadannan idan aka zo zaben fidda gwanin,"

"Zamu ba kowanne dan takara dama iri daya don gwada farin jininsa. Zamu kwacewa duk wani yunkuri na toshe wata kafa a siyasarmu," Ikahriake ya ce.

"A don haka ne, muke sanar da dakatar da Gwamna Godwin Obaseki, Hon Philip Shuaibu da Osarodion Ogie daga jam'iyyar. Muna kuma kira ga kwamitin aikin jam'iyyar nan na kasa da su ladaftar dasu akan laifukansu," ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel