IGP ya daure mahaifina saboda aurena da abokinsa ya mutu - Wata mata ta koka

IGP ya daure mahaifina saboda aurena da abokinsa ya mutu - Wata mata ta koka

Nasiba, diyar Sani Dauda, tsohon shugaban kamfanin motocin Peugeot a Najeriya, ta ce babban sifeton rundunar 'yan sandan Najeriya (IGP), Mohammed Adamu, da cin zarafin iyayenta.

Da take magana da jaridar TheCable a ranar Talata, Nasiba ta ce rundunar 'yan sanda na muzguna wa iyayenta ne saboda ta ki yarda ta cigaba da zama da mijinta da kotu ta raba aurensu. Bazawarar ta yi zargin cewa tsohon mijinta aboki ne wurin IGP Adamu.

Ta ce tun bayar rabuwarsu da tsohon mijinta bata yi magana da wani ba sai ranar Litinin da wasu jami'an 'yan sanda suka zo suka kama mahaifinta da babban yayanta.

Jaridar TheCable ta tuntubi rundunar 'yan sanda domin jin ta bakinsu a kan zargin da Nasiba ke yi wa shugabansu.

A cewar ta, 'yan sandan da suka kama mahaifinta da yayanta sun yi hakan ne bisa umarnin shugabansu, IGP Adamu, kuma basu gabatar da wata shaidar samun izinin kama su ba a lokacin da suka zo gidansu domin tafiya da su.

"Sun zo mana har gida na tare da wata shaida da ke nuna cewa sun samu izinin kama su, sun gabatar da wata takardar korafi ne da tsohon mijina ya rubuta," a cewarta..

Sannan ta cigaba da cewa, "tsohon mijina ya shigar da korafin cewa mahaifina ya dauke ni daga gidansa tare da aurar da ni ga wani mutum daban. Babu gaskiya a cikin zargin da yake yi. Kotu ce ta raba aurenmu kuma ina da takardar shaidar mutuwar aurenmu.

"Toshon mijina yana son cin mutuncina da na dangina. IG ya aiko da motocin 'yan sanda guda biyar su kama mahaifina, da lauyansa da kuma alkalin da ya raba aurenmu. Sun so kama ni tare da sabon mijina, amma bama nan a lokacin."

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun dakile harin da 'yan fashi suka kai bankin CBN

Nasiba ta kara da cewa kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna, Ali Aji Janga, ya taba kiran mahaifinta tare da sanar da shi cewa IG ya bashi umarnin ya kama shi saboda wani korafi da aka rubuta a kansa tare da bayyana cewa har yanzu mahaifinta yana tsare a wurin 'yan sanda.

"Ban san me yasa IG ke tuhumar mahaifina kamar wani dan ta'adda ba. Na san cewa tsohon mijina abokinsa tun yarinta, zai iya aura masa daya daga cikin 'ya'yansa idan ba ya son ganinsa ba mata," a cewar Nasiba.

Frank Mba, kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, ya dauki alkawarin cewa zai gudanar da bincike a kan lamarin bayan jaridar TheCable ta tuntube shi.

Yakubu Sabo, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ya ce yana halarta wani taro, a saboda haka ba zai iya cewa komai a kan lamarin ba tunda baya gari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel