Yan bindiga sun kashe magajin garin wani kauye, sun sanya ma jama’a haraji

Yan bindiga sun kashe magajin garin wani kauye, sun sanya ma jama’a haraji

Wasu gungun miyagu yan bindiga dadi sun kaddamar da wata mummunan hari a kauyen Boni/Anzourou dake Sakoira cikin yankin Tillabery na kasar Nijar dake makwabtaka da Najeriya, inda suka kashe magajin garin.

Rahoton BBC Hausa ya tabbatar da lamarin, inda yace a yanzu haka yan bindigan sun kwace ikon garin bayan kashe magajin garin, kuma sun daura haraji a kan dukkanin al’ummar garin, wanda hakan ya tilasta ma wasu mazauna garin tserewa.

KU KARANTA: Matsalar tsaro: An fara yi ma bakin haure rajista a jahar Sakkwato

Majiyarmu ta bayyana cewa wannan hari na daga cikin alamun dake nuna tsananin tabarbarewar tsaro a kasar Nijar, inda kungiyoyin miyagun yan bindiga suke kai farmaki a kan jami’an tsaro da kuma fararen hula a koda yaushe.

Ko a Najeriya ma an samu wasu miyagun yan bindiga masu garkuwa da mutane da suka halaka wani mutumi mai suna Hamza Abubakar Mahuta bayan sun karbi kudin fansa daga hannun yan uwansa, kudin da ya kai naira dubu 500.

Hamza Mahuta jami’i ne hukumar kula da dokokin hanya ta jahar Kaduna, wanda yan bindigan suka yi awon gaba da shi a ranar 16 ga watan Oktoba a kan hanyar Birnin Gwari yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gida wajen iyalansa.

Jim kadan bayan sun dauke shi, yan bindigan sun nemi a biyasu kudin fansa naira miliyan 5, sai dai sakamakon iyalan nasa sun gaza hada wannan makudan kudi, sai yan bindigan suka kashe shi.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da aikin tantancewa tare da yi ma bakin haure mazauna jahar Sakkwato rajista tare da hadin gwiwar hukumar kula da shige da fice ta Najeriya.

Gwamna Tambuwal ya bayyana aikin a matsayin wanda ya kamata duba da matsalolin tsaron da ake yawan samu a jahar da sauran sassan kasar Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel