Gwamna ya raba motocin alfarma da kujerun Makkah ga mahaddata Al-Qur’ani

Gwamna ya raba motocin alfarma da kujerun Makkah ga mahaddata Al-Qur’ani

Gwamnan jahar Yobe, Mai Mala Buni ya bada kyautukan motocin alfarma da guraben aikin Hajji ga mahaddatan da suka yi zarra a gasar haddar Al-Qur’ani na jahar da hukumar ilimin larabci da ilimin addinin Musulunci ta jahar ta shirya.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito mahaddata daga kananan hukumomin jahar 17 ne suka fafata a gasar, yayin da zakaran gasar zai wakilci jahar a babban gasar haddar Al-Qur’ani ta kasa da kasa da za’a yi a jahar Legas.

KU KARANTA: Matsalar tsaro: An fara yi ma bakin haure rajista a jahar Sakkwato

Alaramma Maina Muhammad daga karamar hukumar Machina ne ya lashe gasar a fannin haddar izu 60 tare da Tajwidi a barayin maza, yayin da Alarammiya Halima daga karamar hukumar Damaturu ta zamto ta daya a bangaren haddar Mata.

Da wannan ne Gwamna Buni ya baiwa kowanne daga cikinsu kyautar sabuwar mota fil kirar Toyota, da kuma kujerar aikin Hajji, kamar yadda wakilin gwamnan a wajen taron, kuma mataimakin gwamnan jahar, Idi Gubana ya bayyana.

Gwamnan ya yi kira ga Musulmai da su kasance masu zuba jari a hanyar Allah ta hanyar kyautatawa tare da taimaka ma jama’a. “Ya kamata mu kasance Musulmai na kwarai ta hanyar danganta kawunanmu da kyawawan koyarwa addinin Musulunci.”

Haka zalika gwamnan ya nemi mahaddatan da suka samu nasara da su dage wajen kare kambun jahar a babban gasar Qur’ani na kasa dake karatowa domin su samu daman wakiltar Najeriya a matakin kasa da kasa.

“Kwazon da kuka nuna zai kara ma dalibai masu tasowa kwarin gwiwa, kuma daga nan burinmu na kasancewa babbar cibiyar karatun addinin Musulunci a Najeriya zai tabbata. Su kuma wadanda basu samu nasara ba, ina basu hakuri, tare da kira a garesu dasu dage nan gaba.” Inji shi.

Daga karshe shugaban hukumar da ta shirya gasar, Mohammed Gujba ya bayyana godiyarsa ga gwamnan jahar Yobe tare da al’ummar jahar gaba daya bisa gudunmuwar da suke basu wanda ya kai nasarar shirya gasar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel