Yanzu Yanzu: Yan sanda sun harbawa dandazon jama’a barkonon tsohuwa a majalisar dokokin Yobe

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun harbawa dandazon jama’a barkonon tsohuwa a majalisar dokokin Yobe

Rundunar yan sandan Najeriya ta watsa wa wasu dandazon jama’a barkonon tsohuwa a majalisar dokokin jihar Yobe.

Lamarin ya afku ne jim kadan bayan Gwamna Mai Mala Buni ya shiga zauren majalisar dokokin jihar domin gabata da kasafin kudinsa na farko a gaban majalisar a matsayin Gwamnan jihar Yobe.

Jim kadan bayan isowar Gwamna Buni majalisar, sai yan sandan suka gaza daidaita dandazon jama’ar da suka biyo gwamnan. Da dama daga cikinsu sun yi kokarin shigewa zauren majalisar tare da gwamnan yayinda yan tsirarun jami’an yan sanda da ke bakin aiki suka gaza daidaita su.

Hakan ya sanya suka kasance da rashin zabi da ya wuce harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa dandazon.

A wani labari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da Sufeto janar na yan sanda, Muhammed Adamu, Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, tare da kwamishinonin zabe na kasa, a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba sun sha barkonon tsohuwa yayinda yan sanda ke kokarin kwantar da wani hargitsi.

Saura kiris a shiga taron yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin jam’iyyun siyasa da 'yan takararsu wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta shirya, tare da manyan jami’an yan sanda, amma ya tarwatse lokacin da wasu da ake zargin yan daban jam’iyya mai mulki ne, suka hana yar takarar gwamna na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Natasha Akpoti, shiga ajen taron ta karfin tuwo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel