Jami’an NNPC su na hada-kai da Tsageru wajen satar mai - Majalisa

Jami’an NNPC su na hada-kai da Tsageru wajen satar mai - Majalisa

Hukumar NAN ta rahoto Majalisar dattawa ta na zargin jami’an kamfanin man Najeriya watau NNPC da kuma kamfanin da ke adana mai, da hada-baki da masu fasa bututun mai kasar.

Kamar yadda mu ka samu labari a yau, 13 ga Watan Nuwamban 2019, majalisar ta fahimci wannan ne a sakamakon wani bincike da kwamitinta ya yi bayan layin mai ya yi bindiga kwanakin baya.

Shugaban kwamitin, Sanata Ibrahim Gobir ya ce NNPC da NPSC su na sane da fashewar bututun Komkom tun kafin hadarin da ya auku ya faru, amma su ka ki daukar matakin da ya dace.

Shugaban majalisar dattawan, Ahmad Lawan, ya bada umarni ga kwamitin da ke kula da sha’anin mai na karkashin kasa ya gayyaci kamfanin NNPC domin ganin yadda za a magance matsalar.

Ahmad Lawan ya kuma bayyana cewa za a hukunta duk wadanda aka samu da hannu wajen wannan danyen aiki. A yunkurin shawo kan matsalar, za a yi wa dokar NOSDRA garambawul.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa ta yi na'am da mikawa Jihar Kogi Biliyan 10

“Kwamitin mu na mai ya gayyaci NNPC da nufin jin irin kokarin da su ka yi a shekarun nan tare da kuma fada mana matakan da su ke dauka; kuma mu ji ko akwai bukatar sake duba lamarin.”

“Wata badakala ce ta ba biliyoyin Daloli, taka-nas mutane su yin wannan barna, ba wai hadari ba ne. Masu zuwa kalar danyen man da ya zauba, su ne su ke rasa rayukansu a karshe.” Inji Lawan.

Rochas Okorocha ya yi Allah-wadai da wannan danyen aiki da ake yi inda ya kira gwamnatin tarayya ta nemi kamfanonin da ake ba kwangilar wannan aiki su rika lura da bututun mai.

Sanata Ibikunle Amosun ya zargi NNPC da hada-baki da masu fasa bututun mai wanda hakan ya kawo tattalin arzikin Najeriya cikas. Ibrahim Musa da wasunsu sun yi magana kan batun.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel