Zaben Kogi: Akwai wani makirci da ake kullawa na dage zabe – PDP ta yi zargi

Zaben Kogi: Akwai wani makirci da ake kullawa na dage zabe – PDP ta yi zargi

Kungiyar kamfen din jam’iyyar People's Democratic Party (PDP) ta yi zargin cewa akwai wani makirci da ake kullawa domin dage zaben gwamnan jihar Kogi da za a yi a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba.

Musamman PDP ta zargi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da gwamnatin jihar Kogi da shirya wannan makarkashiya.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi da mataimakin daraktan labarai na jam’iyyar, Austin Okhai ya aikewa yan jarida a ranar Laraba, 12 ga watan Nuwamba.

Okhai ya bayyana cewa APC da gwamnatin da Yahaya Bello ke jagoranta suna nan suna kamun kafa gabannin zaben.

Ya bayyana cewa PDP ta shirya cewa APC ce za ta zo ta uku a zaben, don haka suke kulla makirci domin jinkirtar da tsarin zaben.

Kungiyar kamfen din ta roki hukumar INEC da kada ta yarda da duk wani yunkuri da zai saba abunda mutanen jihar ke tsammani.

Jam’iyyar ta ce magoya bayanta da masu zabe a fadin jihar sun taso daga wurare da ke nesa da kusa domin samun damar zabar dan takarar PDP.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben Gwamna Emmanuel

Kungiyar ta ce idan har yunkuri ya yiwu toh zai shafi sakamakon zaben.

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto cewa Majalisar dattawan Najeriya ta amince da biyan gwamnatin jihar Kogi kudi bilyan goma ana saura kwanaki biyu zaben gwamnan jihar.

A watan Oktoba, shugaba Muhammadu Buhari ya nemi izinin majalisar dattawa, a wata wasika da ya aika, na biyan gwamnatin jihar Kogi naira bilyan goma na basussukan da suka bin gwamnatin tarayya na gudanar da ayyuka mallakan FG.

An yi cece-kuce a zauren majalisar yayinda Sanatocin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP suka nuna rashin yardarsu da biyan kudin a wannan lokaci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel