Yanzu-yanzu: Ana saura kwana biyu zabe, majalisar dattawa ta amince Buhari ya baiwa gwamnan Kogi N10bn

Yanzu-yanzu: Ana saura kwana biyu zabe, majalisar dattawa ta amince Buhari ya baiwa gwamnan Kogi N10bn

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da biyan gwamnatin jihar Kogi kudi bilyan goma ana saura kwanaki biyu zaben gwamnan jihar.

A watan Oktoba, shugaba Muhammadu Buhari ya nemi izinin majalisar dattawa, a wata wasika da ya aika, na biyan gwamnatin jihar Kogi naira bilyan goma na basussukan da suka bin gwamnatin tarayya na gudanar da ayyuka mallakan FG.

An yi cece-kuce a zauren majalisar yayinda Sanatocin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP suka nuna rashin yardarsu da biyan kudin a wannan lokaci.

DUBA NAN: An saki ASD, 'Dansa, Surukinsa, da Sheikh Murtala Al-Misry

Shugaban marasa rinjaye a majalisar, Sanata Enyinayya Abaribe, wanda yayi magana madadin dukkan sanatocin jam'iyyar ya bukaci majalisa ta dakatad da biyan kudin zuwa mako mai zuwa; bayan an kammala zabe.

Amma shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce sam ba za'a yi hakan ba saboda jihar Kogi ta nemi kudin tun zamanin Saraki amma aka hanasu.

Kalli hirarmu da hadimin Buhari kan kudin da ake shirin ba jihar Kogi

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel