Gab da zabe, Surukin Atiku ya bani $140,000 in kaiwa Obasanjo - Shaida a kotu

Gab da zabe, Surukin Atiku ya bani $140,000 in kaiwa Obasanjo - Shaida a kotu

Bashir Mohammed ya bayyanawa babban kotun tarayya dake Legas ranar Talata cewa Abdullahi Babalele, Surukin tsohon shugaban kasa Atiku, ya baiwa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kudi $140,000 kafin zabe.

Bashir wanda hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gabatar matsayin shaida.

Hukumar na tuhumar Abdullahi Babalele da laifin almundananan $140,000 gab da zaben shugaban kasa a Febrairun 2019.

Za ku tuna cewa Obasanjo ya marawa Atiku baya a zaben shugaban kasan da ya gabata.

Bashir Mohammed ya bayyanawa kotu yadda ya kaiwa Obasanjo kudin a gidansa dake jihar Ogun.

Ya ce a watan Febrairun da aka gudanar da zaben, Babalele ya bukaci aikensa kaiwa Obasanjo wani sako.

DUBA NAN: Mun kama yan Boko Haram 5,475, mun ragargaza masana'antun hada Bam 32

Yace: "Da na isa kofar gidansa, sai wani ya shiga dani inda na gana da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kuma na mika masa sakon."

"Sai na kira Babalele a gaban tsohon shugaban kasa Obasanjo kuma na sanar da shi cewa na isar da sakon. Sai yace yayi kyau."

Alkalin, Chukwujekwu Aneke, ya dage karar zuwa ranar Laraba domin cigaba da karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel