Zaben Kogi: Yan daban APC sun kai mani hari a jihar Kogi – Natasha Akpoti

Zaben Kogi: Yan daban APC sun kai mani hari a jihar Kogi – Natasha Akpoti

Yan kwanaki kafin zaben gwamnan jihar Kogi, yar takarar jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Natasha Akpoti, ta zargi yan iska da ke biyayya ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki da kai mata hari.

A wani bidiyo da Channels Television ta saki, Akpoti ta ce yan daban, wadanda suka halarci wani taron masu ruwa da tsaki a harkar siyasa da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta shirya, sun zazzage ta sunaye na batanci kama irin karuwa sannan suka tureta a kasa.

Ta yi zargin cewa mafi akasarin yan daban wadanda ke sanye da kaya mai rubutun GYB – wani inkiya da ake amfani da shi wajen kiran gwamnan jiha Kogi, Yahaya Bello, sun kuma yi barazanar cewa ba za a bari ta shiga wajen taron da ake gudanarwa ba.

“A hanyarmu na zuwa halartan taron masu ruwa da tsaki na siyasa da INEC ta shirya... yan daban APC sun kai mani hari sannan suka tozarta ni,” in ji Akpoti.

Yayinda ta fashe da kuma a cikin wai bidiyo da Legit.ng ta gani, Akpoti ta bayyana cewa koda dai akwai jami’an yan sanda da dama da wasu jami’ai sama da 500 daga sauran hukumomin tsaro sanye da inifam daban-daban, yan daban na ta far mata da hari ta hanyar bugu da tozarci.

A cewarta, jami’an tsaron na kallo yayinda ake cin zarafinta ba tare da sun hana yan iskan daga cigaba da tozarta ta ba.

KU KARANTA KUMA: Rufe iyakokin Najeriya: Majalisa ta bukaci Kwastam da ta dakatar da batun haramta raba mai ga wasu garuruwa

Da ya ke martani akan ikirarin Akpoti, Shugaban labarai na kwamitin kamfen din APC a Kogi, Kingsley Fanwo, ya ce jam’iyya ba ta da yan daba kamar yadda yar takarar ta SDP ta yi zargi.

Fanwo ya ce APC ba ta bukatar amfani da yan daba don cin zabe a jihar dama fadin kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel