Mun kama yan Boko Haram 5,475, mun ragargaza masana'antun hada Bam 32

Mun kama yan Boko Haram 5,475, mun ragargaza masana'antun hada Bam 32

Akalla yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram 5,475 ne jami'an hukumar Sojoji suka kama yayinda suka hallaka dubunnai, babban hafsan hukumar Soji, Laftanan Janar Tukur Buratai ya bayyana.

Buratai ya bayyana hakan ne a taron karrama hukumomin tsaro da ya gudana a birnin Dubai, kasar UAE.

Buratai wanda ya samun wakilcin shugaban shirye-shiryen hukumar, Laftanan Janar Lamidi Adeosun, ya ce hukumar ta ragargaza masana'atun hada bama-bamai 32 na Boko haram.

A cewarsa, an nakasa yan ta'ddan matuka saboda an rage yawansu daga 35,000 zuwa kasa da 5000, wanda ke nuna cewa an kayar da su.

Ya gabatar da jawabi mai taken: "Matsayar hukumar sojin Najeriya wajen yakan rashin tsaro a ciki da wajen Najeriya."

Buratai yace: "An kashe dubunnan yan ta'adda, an damke 5,473 kuma an lalata masana'antun hada bama-bamai 32."

"Bugu da gari, a rage yawa yan ta'addan matuka zuwa kasa da 5,000 sabanin kimanin 35,000."

"Hakazalika hukumar Sojoji sun yi rashin Sojoji da hafsoshi yayin wannan yakin da ya zama kalubale ga kasar. Lallai, dubi ga irin kokarin Sojin Najeriya, muna samun nasara kan Boko Haram."

DUBA NAN: Gab da zabe, Surukin Atiku ya bani $140,000 in kaiwa Osinbajo - Shaida a kotu

Buratai ya ce lissafi daga hukumar kai agaji na gaggawa NEMA ya nuna cewa Boko Haram sun kashe mutane 30,000 zuwa 100,000, kuma sun kora mutane milyan biyu daga muhallansu.

Mutanen a halin yanzu na zaune a sansanin yan gudun hijra 35 sun kai 200,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel