Rufe iyakokin Najeriya: Majalisa ta bukaci Kwastam da ta dakatar da batun haramta raba mai ga wasu garuruwa

Rufe iyakokin Najeriya: Majalisa ta bukaci Kwastam da ta dakatar da batun haramta raba mai ga wasu garuruwa

Majalisar wakilai a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba, ta bukaci hukumar kwastam na Najeriya da ta dage haramci kan raba man fetur ga tashoshin mai a garuruwa da biranen da ke tsakanin kilomita 20 da iyakokin kasar.

Majalisar a wani korafi da dan majalisa Sada Soli ya ce haramcin na haifar da matsi ga rayuwar mutane a wadannan garuruwa na iyakokin, ciki harda yan Najeriya.

A cewar Soli, umurnin da shugaban kwastam din ya bayar ya kara da dokar hukumar da kuma na shirin.

Sauran yan majalisar da suka marawa Soli baya sun yarda cewa tuni dama rufe iyakokin ya uzurawa rayuwar mutanen wadannan garuruwan sannan hana su man fetur sunce zai dada tabarbarar da lamarin.

Hukumar kwastam a kokarinta na magance fasa kauri ta sanya haramci kan siyar da fetur a tsakanin kilomita 20 na iyakokin kasar.

Shugaban hukumar kwastam, Kanal Hameed Ali (mai ritaya) a makon da ya gabata ya yi umurnin cewa kada a ba kowani gidan mai da ke tsakanin kilomita 20 da iyakokin kasar man fetur.

Idan ba za ku manta ba a baya mun ji cewa kwanaki biyar bayan umarnin da gwamnatin tarayya ta bada na hana kai man fetur garuruwa masu kilomita 20 kusa da iyakokin kasar nan, mazauna garuruwan kusa da iyakokin kasar nan irinsu jihohin Ogun, Legas, Adamawa, Katsina da Sokoto sun fara kukan illar da wannan umarnin ya aka bada.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe Shugaban makarantar Taraba sabon hari da suka kai Wukari

Jaridu da dama sun ruwaito yadda hukumar kwastam ta kasa ta bada sanarwar cewa gwamnatin tarayya ta haramta kai man fetur duk gidajen mai da ke da nisan kilomita 20 zuwa iyakokin kasar nan.

Kamar yadda rahoto ya nuna, jihohin Ogun, Legas, Adamawa, Katsina da Sokoto sun fara fadawa mummunar matsalar rashin man fetur tare da tashin gwauron zabi da yayi a yankunan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel