Ka shirya taron shuwagabannin jam'iyya ko ka ajiye aiki - Gwamnonin APC ga Oshiomhole

Ka shirya taron shuwagabannin jam'iyya ko ka ajiye aiki - Gwamnonin APC ga Oshiomhole

Gwamnonin da aka zaba karkashin inuwar jam'iyyar APC sun nuna rashin jin dadinsu akan rikicin da ke cin jam'iyyar. Sun bukaci shugaban jam'iyyar na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole da ya shirya taron shuwagabannin jam'iyyar da gaggawa ko ya sauka daga kujerarsa.

Kungiyar gwamnnoni ta bada wannan sanarwar ne sakamakon rikicin siyasar da ke tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da Oshiomhole daga cikin sauran rikice-rikicen jam'iyyar a fadin kasar nan.

Idan zaku tuna, a jiya Talata ne Legit.ng ta ruwaito yadda jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole a jihar akan zarginsa da hannu dumu-dumu a rikicin jam'iyyar na jihar.

Hukuncin kuwa ya biyo bayan kuri'un da shuwagabannin jam'iyyar na kananan hukumomi 18 na jihar suka kada akan dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa a jihar.

Takardar da aka ba manema labari a yau Laraba a garin Abuja, ta samu sa hannun daraktan kungiyar gwamnonin na, Salihu Moh. Lukman inda kungiyar ta bukaci amsar tambayoyin nan. "Mene ne dalilin da ya hana taron shuwagabannin jam'iyya ko kuma taron jam'iyya wanda yakamata a yi duk watanni hudu? Akan mene wasu sassan jam'iyyar a karkashin mulkin Oshiomhole zasu cigaba da fuskantar irin wadannan matsalolin?"

DUBA WANNAN: Kotu ta yi barazanar fatali da shari'ar tsohuwar ministar man fetur

"Mene ne Oshiomhole ke fatan cimmawa a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa bayan baya wani yunkurin habaka jam'iyyar?"

A yayin da akwai bukatar taron shuwagabannin jam'iyyar, gwamnoni sun ce: "A halin da ake ciki yanzu, babu abinda zai shawo kan matsalar nan da ta wuce taron shuwagabannin jam'iyyar nan. Ko Oshiomhole ya mutunta kundin tsarin mulkin jam'iyyar nan kuma ya hada taro don shawo kan kalubalen da jam'iyyar ke fuskanta ko kuma ya rungumi cewa ba zai iya tafi da lamurran jam'iyyar nan ba ya ajiye aiki." in ji takardar.

Dole ne shuwagabanninmu na kasa su tashi tsaye don ganin sun kawo karshen kalubalen da jam'iyyar nan ke fuskanta. Hakan cin fuska ne ga jam'iyyar a idon duniya, in ji kungiyar.

Gwamnonin sun ce abun da kunar rai a matsayinsa na wanda ya gogar dasu a harkar siyasa amma ya tsunduma a siyasar bangare, hakan ragewa kai kima ne da daraja a matsayinsa na shugaban jam'iyyar na kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel