Kotu ta yi barazanar fatali da shari'ar tsohuwar ministar man fetur

Kotu ta yi barazanar fatali da shari'ar tsohuwar ministar man fetur

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba wa hukumar yaki da rashawa ta EFCC wa'adin kawo tsohuwar ministar man fetur, Mrs. Diezani Alison-Madueke gaban kotun.

Kotun ta ba wa hukumar wa'adin zuwa watan Maris na shekarar 2020 da su san yadda za su yi su kawo tsohuwar ministar Najeriya daga UK.

A watan Nuwamba na shekarar 2018 ne hukumar yaki da rashawa ta EFCC din ta mika kokenta gaban kotun akan zargin ministar da take da laifuka 13.

Laifukan sun hada da zargin ministar da ake da mallakar kudade hara dala miliyan 39.7 da kuma naira biliyan 3.32 wanda ake zargin ta siya kadarori a jihohin Abuja, Legas da Fatakkwal a jihar Rivers, yayin da take ministar man fetur din kasar nan.

DUBA WANNAN: Kano: An gurfanar da ma'aikatan kotun shari'a kan damfarar miliyoyin naira

Yayin da aka koma cigaba da shari'ar, Jastis Ijeoma Ojukwu ta yi barazanar fatali da karar akan almundahanar kudaden matukar hukumar yaki da rashawan ta kasa kawo wacce ake zargin kotun nan da watan Maris na shekarar 2020.

Lauyan masu karar, Faruk Abdullahi, ya bukaci kotun ta dage shari'ar har illa masha'Allahu. Sun bukaci hakan ne kuwa sakamakon kalubalen da hukumar yaki da rashawar take fuskanta a yunkurin samun dawo da tsohuwar ministar gida Najeriya.

Diezani dai ta share waje tayi zamnata ne a kasar Ingila ne tun bayan da aka fara bincike akan almundahanar kudaden da ake zarginta dashi a 2015 bayan da ta sauka daga bar ofishin a matsayin ministar man fetur din kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel