Goal 50: ‘Dan bayan Liverpool, Virgil van Dijk, ya lashe kyautar 2019

Goal 50: ‘Dan bayan Liverpool, Virgil van Dijk, ya lashe kyautar 2019

Virgil van Dijk ya zama ‘dan wasan bayan da ya fara lashe kyautar Goal 50 a wannan shekarar. Kokarin ‘Dan kwallon na Liverpool ta sa Goal.com ta zabe sa a matsayin Gwarzon shekara.

Kamar yadda mu ka samu labari daga shafin kwallon kafa na Goal.com, an zabi ‘yar wasar kasar Amurka Megan Rapinoe mai shekaru 34 a matsayin Gwarzon ‘yan wasan mata na Duniya.

Megan Rapinoe ta zuba kwallaye shida a gasar cin kofin Duniya na mata da aka yi inda ta kai Amurka zuwa ga nasara. Rapinoe ta kuma yi sanadiyyar cin kwallaye uku a gasar na bana.

‘Dan wasa Virgil van Dijk mai shekaru 28 da haihuwa ya kerewa Lionel Messi da kuma Cristiano Ronaldo a gasar wannan shekara bayan Liverpool ta lashe gasar cin kofin Nahiyar Turai.

‘Yan wasan Liverpool uku ne su ka shigo cikin Taurari biyar na farko na Goal 50 na bana. Lionel Messi na Barcelona da ‘Dan wasan Juventus, Cristiano Ronaldo ne kurum bare a cikinsu.

KU KARANTA: Isa Ali Pantami ya hadu da 'Dan wasan Liverpool a Misra

Mohamed Salah shi ne ya zo na uku a jerin bayan Lionel Messi , kuma gaban Cristiano Ronaldo. ‘Dan wasan gaban Liverpool, Sadio Mane, shi ne ya cike gurbin biyar din sahum farko.

Ana tunanin cewa duk Duniyar kwallon kafa babu kwararren ‘dan wasan baya da ya ke tashe irin Van Dijk a yanzu. Shekarun baya da su ka wuce Liverpool ta sayo shi daga Southampton.

Duk da irin zuba kwallayen da Mohammed Salah da Sadio Mane su ke yi a Liverpool, Masana na cewa Van Dijk shi ne ‘dan wasan da ya fi kowane amfani da tasiri wajen nasarar kungiyar.

‘Dan wasan ya ce ya ji dadin lashe wannan kyauta. ya ce abu ne na musamman ya yi fice cikin ‘yan kwallon Duniya. Kila nan gaba ya shiga cikin manyan ‘yan wasan da aka taba yi a tarihi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel