Masu garkuwa sun kashe jami’in gwamnatin jahar Kaduna bayan sun amshi kudin fansa

Masu garkuwa sun kashe jami’in gwamnatin jahar Kaduna bayan sun amshi kudin fansa

Miyagun yan bindiga masu garkuwa da mutane sun halaka wani mutumi mai suna Hamza Abubakar Mahuta bayan sun karbi kudin fansa daga hannun yan uwansa, kudin da ya kai naira dubu 500, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyarmu ta ruwaito Hamza Mahuta jami’i ne hukumar kula da dokokin hanya ta jahar Kaduna, wanda yan bindigan suka yi awon gaba da shi a ranar 16 ga watan Oktoba a kan hanyar Birnin Gwari yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gida wajen iyalansa.

KU KARANTA: Yaki da ta’addanci: Dakarun Sojan sama sun tarwatsa mafakar Boko Haram, sun kashe da dama

Masu garkuwa sun kashe jami’in gwamnatin jahar Kaduna bayan sun amshi kudin fansa
Mahuta
Source: Facebook

Jim kadan bayan sun dauke shi, yan bindigan sun nemi a biyasu kudin fansa naira miliyan 5, sai dai sakamakon iyalan nasa sun gaza hada wannan makudan kudi, sai yan bindigan suka kashe shi.

Wani dan uwan mamacin da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da cewa yan bindigan ne suka fada musu cewa sun kashe Hamza, amma har yanzu basu basu gawarsa ko su fada musu inda suka jefar da gawar tasa ba.

“Hamza dan uwana ne, kuma a ranar Litinin aka sanar mana da mutuwarsa da misalin karfe 5:30 na yamma bayan iyalansa sun biya N500,000 kudin fansa ga masu garkuwan. Mun samu labarin tun kwanaki 9 da suka gabata suka kashe shi.

“Amma sai suka yi ta kiranmu suna mana karyar cewa ba zasu sake shi ba sai mun biya kudin fansa, bayan da suka karbi kudin ne sai suka bayyana mana cewa sun kashe Hamza, amma ba zasu bamu gawarsa ba.” Inji shi.

Sai dai ko da majiyarmu ta yi kokarin jin ta bakin mataimakin manajan hulda da jama’a na hukumar KASTELEA, Joy George Zemo, sai yace ba zasu iya cewa komai game da batun ba saboda basu da cikakken bayani.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da aikin tantancewa tare da yi ma bakin haure mazauna jahar Sakkwato rajista tare da hadin gwiwar hukumar kula da shige da fice ta Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel