Kano: Hango shan kashi a kotu ya sa PDP ta kideme – Gwamnatin Kano

Kano: Hango shan kashi a kotu ya sa PDP ta kideme – Gwamnatin Kano

APC mai mulki a jihar Kano, ta yi kaca-kaca da jam’iyyar hamayya ta PDP a kan wani kuka da ta fara yi na cewa gwamnati na kokarin sauya Alkalan da za su saurari karar shari’ar jihar.

Kamar yadda mu ka samu labari, gwamnatin Kano ta karyata zargin da PDP ta ke yi inda ta ce ana kokarin gogawa Alkalan baki ne. Kwamishinan yada labaran jihar, shi ya wannna jawabi jiya.

A Ranar Talata, Malam Muhammad Garba, ya fadawa Jaridar This Day cewa PDP ta kidime ne, kuma ta rude, ta na jin tsoron yiwuwar sake shan kashi a gaban kotun daukaka karar zaben jihar.

A jawabin da Garba ya fitar Ranar 12 ga Watan Nuwamban 2019, ya nuna cewa ko da an sauya Alkalan da za su saurari karar, kotu ta na da hurumin zaben Alkalanta da za su karbi wani korafi.

Jawabin Kwamishinan ya ce babban makasudi shi ne gaskiya ta yi halinta a shari’ar, inda ya ce tun ba yau ba, jam’iyyar PDP ta yi fice wajen yada karyayyaki yayin da duk ake gaban kuliya.

KU KARANTA: Gwamnan Katsina ya ba Alkalai kudi domin a murde zabe - NCP

Mai girma Kwamishinan ya ke cewa: “Jam’iyyar hamayyar ta yi irin wannan a lokaci da ake shari’ar sauraron korafin zaben gwamnan jihar Kano da kuma karar zaben shugaban kasa.”

Garba ya kara da cewa: “Abin takaici ne ace jam’iyyar adawar da ta shigar da kara ta hanyar da ta dace a kotu za ta buge da katobara har ta kai ta na jefawa kuliya zargin da ba su da tushe.”

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa: “Ba laifi ba ne don ‘Ya ‘yan APC sun nuna gamsuwarsu game da yadda shari’ar za ta kaya, amma ‘yan takararta ba su da niyyar tsoma baki a shari’a.”

A karshen jawabin, Kwamishinan ya yi gargadi cewa gwamnatin jihar Kano ba za ta amince da wasu kalamai ko abubuwa da za su iya tunzura jama’a su kai ga kawo hatsaniya a cikin al’umma.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel