Buhari: Osinbajo ya tashi aiki kenan – Tsohon Mukarrabin Shugaban kasa

Buhari: Osinbajo ya tashi aiki kenan – Tsohon Mukarrabin Shugaban kasa

Bayan tarka-tarkar da ake ta yi a fadar shugaban kasa tsakanin bangaren Mai girma shugaban kasa da mataimakinsa, mun samu wani wanda ya san fadar shugaban kasar ya yi mana tsokaci.

Wani tsohon Hadimi a fadar shugaban kasa, Umar Sani, ya yi wata hira ta musamman da Legit.ng inda ya bayyana mana cewa kila nan gaba a karbe duk ikon da dokar kasa ta ba Yemi Osinbajo.

Umar Sani wanda ya yi aiki a matsayin Mai ba tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, shawara ya bayyana cewa babu shakka akwai wasu a fadar Aso Villa da ke gara Osinbajo.

A cewarsa, cire mataimakin shugaban kasar daga bakin aikinsa da wasu matakan da gwamnatin tarayya ta dauka ya nuna cewa akwai matsala tsakanin Muhammadu Buhari da mataimakinsa.

“Idan ba rami mai ya kawo batun rami, ba za a rika daukar tsauraran matakai haka nan babu dalili ba. A da an kyale VP ya na aikinsa kalau, sai kwatsam aka ce yanzu sai ya nemi izni.

KU KARANTA: Ashe Mamman Daura bai da wani iko a Gwamnatin Buhari

Sani ya ke cewa: “An ruguza kwamitin da ke binciken kadarorin gwamnati da ke hannun jami’ai wanda ya ke karkashin ofishin mataimakin shugaban kasa sannan kuma an karbe wasu aikinsa.”

:"An maida wasu nauyin da aka san mataimakin shugaban kasar da su zuwa ma’aikatar bada agajin gaggawa da cigaban zamantakewa. "Inda tsohon Hadimin ya ke magana kan ofishin N-SIP.

"Taron da aka yi a fadar Sarkin Ife inda Ministan harkokin gida ya wakilci Mai girma shugaban kasa duk da Yemi Osinbajo ya na wurin da kansa ya nuna cewa akwai rina a kaba." inji Sani.

Daukar kudiri da aka yi har zuwa Landan domin shugaban kasa ya sa hannu tare da sallamar Hadiman mataimakin shugaban kasar 35 ya nuna cewa Osinbajo ba zai sake tsayawa Buhari ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel