Kotun daukaka kara ta sake tsige wani dan majalisa na APC a Kwara

Kotun daukaka kara ta sake tsige wani dan majalisa na APC a Kwara

Kotun daukaka kara da ke zama a Ilorin, a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba, ta kaddamar da dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a mazabar Ilorin ta Kudu, Hon. Abdulraheem Agboola a matsayin ainahin zababben dan majalisar dokokin jihar.

Justis Hamman Barkar Hkawu ne ya zartar da hukunci inda ya dakatar da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Abdulazeez Oluwanilo, sannan ya umurci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC ) da ta ba dan takarar PDP takardar shaidar cin zabe.

Kotun ta yanke hukunci kan hargitsin zaben fidda gwani na APC wacce ta gabatar da Alhaji Suleiman Abdulsalam wanda aka fi sani da Cement amma daga bisani ta sauya shi da Abdulazeez Oluwanilo mai shekara 28.

Kotun daukaka karar ta riki cewa APC bata da sahihin dan takara a mazabar don haka ta kaddamar da dan takara na biyu da ke da kuri’u mafi yawa, wanda ya kasance na PDP, Abdulraheem Agboola a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.

Dan takarar na PDP ya kalubalanci cancantar dan takarar APC da tsarin zaben jam’iyyarsa a kotun zabe.

Idan za a tuna kotun sauraron kararrakin zaben da farko ta yi umurnin sake sabon zabe a mazabar Ilorin ta Kudu a majalisar dokokin jihar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: An kashe yan sanda 2 a Bayelsa

A halin da ake ciki, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Rt. Hon Ali Ahmad, wanda ya wakilci mazabar Ilorin ta Kudu tsawon shekaru takwas a majalisar dokokin jihar ya taya Agboola murna, inda ya bayyana cewa zai kasance daya daga cikin manyan mambobin majalisar.

A wai labari na daban, mun ji cewa Jam'iyyarr APC reshen jihar Edo ta sanar da dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, bisa zarginsa da hannu a rikicin da APC ke fama dashi a jihar.

Jam'iyyar ta yanke shawarar dakatar da OShiomhole ne biyo bayan kada kuri'ar rashin amince wa da shi da shuwagabannin jam'iyyar APC a kananan hukumomi 18 a jihar Edo suka yi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel