An yiwa yara 99 da suka shafe kwanaki 40 ba su rasa sallah a jam'i ba kyautar kekuna

An yiwa yara 99 da suka shafe kwanaki 40 ba su rasa sallah a jam'i ba kyautar kekuna

- Wani masallaci a Banglore ya ba yaran da suka halarci sallar asuba na kwanki 40 a jere kyautar kekuna

- Kwamitin masallacin ya samu yara 99 da suka cike wa'adin inda 14 kuma suka yi kwanaki 35 suna samun jam'in sallar asubar

- Masallatai da yawa sun fara daukar wannan salon don karfafawa yara guiwa don tashin sallar asubar

Masallacin Hajee Sir Ismail Sait da ke birnin Frazer a Banglore ya ba wa kananan yaran da suka yi kwanaki 40 a jere suna zuwa sallar asuba kyautar kekuna.

An bada wannan sanarwar ne a masallacin Banglore din ne don karfafa guiwar yara wajen zuwa sallar asuba a jam'i.

Kwamitin da ya shirya yayi koyi ne da masallatan kasashen Turkiyya da Misra.

Sun yi amfani da irin wannan dabarar ne don karfafawa yara guiwa wajen fitowa sallar asuba a jam'i.

Kamar yadda kwamitin masallaci suka sanar, yara 99 ne suka samu hakartar sallar asubar a jam'i na kwanaki 40 inda yara 14 ne suka samu sallar asubar a jam'i na kwanaki 35.

KU KARANTA: Deen Mohammed: Dattijon da sanadiyyarsa sama da mutane dubu 100 suka Musulunta shekaru kadan da komawarsa Musulunci

Kwamitin masallacin su ba yara 99 kyautar kekekuna inda suka ba sauran agogon hannu.

Bayan nan, kwamitin masallacin ya samu sunayen yara sama da 200 wadanda suka yi niyyar halartar sallar asubar a jam'i.

A wannan karo kwamitin masallacin yayi alkawarin bada kyautar kayan motsa jiki. Masallatai da yawa kuwa sun rungumi wannan salon don karfafawa yara kanana guiwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel