To fah: Wani saurayi ya koka akan yadda 'yan sanda suka yi kunnen uwar shegu da shi bayan 'yan mata uku sun yi masa fyade

To fah: Wani saurayi ya koka akan yadda 'yan sanda suka yi kunnen uwar shegu da shi bayan 'yan mata uku sun yi masa fyade

- Wani saurayi ma'abocin amfani da kafa sada zumunta ta tuwita ya bayyana yadda 'yan mata uku suka yi mishi fyade

- Koda ya sanar da 'yan sanda sai daya daga cikinsu ya shawarce shi da ya koma gida don bai cika namiji ba

- Ya amsa gayyatar daya daga cikin abokannan karatunsa ne inda suka mishi barbade har suka aikata masa aika-aikar

Wani ma'abocin amfani da shafin kafar sada zumunta ta tuwita, @ezemmuo-nkanu ya bada labarin yadda 'yan mata 3 suka yi masa fyade lokacin yana shekara ta biyu a jami'a kuma 'yan sanda suka ki bi masa hakkinsa bayan ya kai rahoto.

Ga labarin kamar haka: "Ina shekara ta biyu a jami'a ne 'yan mata 3 suka yi min fyade. Na kai kara amma babu abinda aka yi musu. Na kasa mantawa da wannan lamari a kwakwalwata don duk ranar 10 ga watan Nuwamba sai na tuna da wannan ranar," ya wallafaa shafinsa.

Ya cigaba da cewa, "Jami'in dan sandan dana kaiwa kara ya ce min saurayi koma gida domin baka cika namiji ba kuma kada ka je kana sanar da cewa mace ta yi maka fyade in ba haka ba kuwa, babu wanda zai mutunta ka."

"Abun ya faru ne lokacin ina da shekaru 21, daya daga cikin abokan karatuna wacce muke matukar shiri ta ja ni, kafin wannan lokacin sau biyu kawai na taba saduwa da mace. Ban taba sanin mace ba sai da na shiga jami'a, a jami'ar ne na yi budurwa har muka sadu sau biyu a zango na biyu na karatuna."

KU KARANTA: Hukunci ko azaba: Wani ya kulle kanwarsa a daki na tsawon shekara biyu a jihar Kaduna

"Yar ajinmu mai suna Rose ta gayyaceni dakinta. Ina isa na tarar da wasu 'yan mata biyu sa'o'inta. An sanar min cewa daya daga cikinsu na bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta. Na taya ta murna inda muka sha abubuwan sha da ciye-ciye,"

"Ina cikin hayyacina amma jikina ya saki. A nan ne suka fara sumbata ta. Nayi yunkurin tashi amma Rose ta maidani. A haka suka yi min fyade. Ina tunanin cikin shinkafar da na ci ne suka zuba min magani. Don sunyi duk abinda suke so da ni."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel