Sai bango ya tsage: An damke dan sanda mai yiwa yan Boko Haram safarar Taramol

Sai bango ya tsage: An damke dan sanda mai yiwa yan Boko Haram safarar Taramol

Hukumar yakin safara da ta'amuni da muggan kwayoyi wato NDLEA ta alanta damke wani jami'in dan sanda da laifin yiwa yan Boko Haram safarar kilo 59 na kwayar Taramol a garin Gwoza, jihar Borno.

Kwamandan NDLEA na jihar Yobe, Reuben Apeh, ya bayyana hakan ne yayinda yake hira da manema labarai a Damaturu, babbar birnin jihar Yobe ranar Talata.

Ya ce an damke dan sandan ne tare da wani mai safarar kwayoyi a ranar 7 ga Nuwamba. Apeh ya ce mutumin ya laburta musu cewa hannun wani jami'in Kwastam yake siya a Legas.

Apeh yace: Ya laburta mana cewa yana amfani da dan sandan wajen kai kwayoyin Maiduguri kafin karasawa Gwoza domin sayarwa yan ta'adda."

"Ya yi ikirarin cewa kwayoyin na cikin kayan da hukumar Kwastam suka kwace a wani kamu da suka a Legas, kuma an sayar masa N6m."

"Har yanzu muna aiki kansa domin samun labarin jami'in kwastam din da wani abokin aikinsu dake Ijora, Legas."

"An dauko kwayoyin daha Legas zuwa Jos, sai aka mikawa dan sanda domin ya kai Maidiguri, sannan shi mutumin zai karasa da su wajen yan Boko Haram."

A shekarar 2018, majalisar dinkin duniya ta nuna damuwarta kan yadda ta'amuni da Taramol da wasu muggan kwayoyi ya yawaita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel