Yanzu-yanzu: An kashe yan sanda 2 a Bayelsa

Yanzu-yanzu: An kashe yan sanda 2 a Bayelsa

An harbe jami'an yan sanda biyu har lahira a garin Otuogidi, karamar hukumar Ogbia ta jihar Bayelsa a ranar Talata, 12 ga Nuwamba, 2019.

Bayan hallakasu, Yan bindigan sun yi awon gaba da makaman yan sandan ana saura kwanaki shida zaben gwamnan jihar da zai gudana ranar Asabar.

An kaiwa yan sandan hari ne a kusa da kwalejin koyan ilmin kiwon lafiya a Ogbia.

Yayinda daya daga cikin yan sandan ya mutu nan take, dayan ya cikasa ne bayan an kaishi asibiti.

Wannan mumunan abu ya biyo bayan Sifeto Janar na hukumar yan sanda, Muhammadn Adamu, ya sanar da cewa za'a tura jami'ai 32,000 jihar domin zabe.

DUBA NAN An damke dan sanda yiwa yan Boko Haram safarar Taramol

A wani labarin daban, Babban kotun tarayya dake zamanta a Abuja ranar Talata ta haramtawa, Biobarakuma Degi, takarar kujeran mataimakin gwamnan jihar Bayelsa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC.

Kotun ta yanke hukuncin ana saura kwanaki shida zabe.

Justice Inyang Ekwo ya yanke hukuncin ne kan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1101/2019 da jam'iyyar Peoples Democratic Party ta shigar.

Za'a gudanar da zaben jihar Bayelsa ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel