Kano: An gurfanar da ma'aikatan kotun shari'a kan damfarar miliyoyin naira

Kano: An gurfanar da ma'aikatan kotun shari'a kan damfarar miliyoyin naira

Ofishin hukumar yaki da rashawa ta EFCC reshen jihar Kano a ranar Talata ya gurfanar da Ado Shehu da Ali Muhammad a gaban Jastis Amina Aliyu ta babbar kotun jihar Kano akan laifuka uku da suka hada da sata.

Mai koken, Sanusi Yakubu, ya zargi cewa, wani Williams Aondo wanda a yanzu ya rasu, ma'aikacin daya daga cikin bankunan zamani, ya hada kai da Shehu da Muhammad, wadanda duk ma'aikatan kotun shari'ar ne inda suka far wa dukiyarsa da ke asusun bankin da tunanin ya rasu. A rashin sanin cewa yana raye amma yana kasar Saudi Arabia ne.

Mai koken ya zargi kotun da amfani da abinda Shehu da Muhammad suka gabatar mata na cewa ya rasu, inda suka bukaci da a kwashe kudinsa don rabawa magada. Hakan kuwa ya auku ne a watan Disamba na 2017.

DUBA WANNAN: NDLEA ta cafke dan sanda da ake zargi da samar wa da 'yan Boko Haram miyagun kwayoyi

Wadanda ake karar sun musanta laifin da ake zarginsu dashi. A don haka nelauyan masu gabatar da kara, Zarami Mohammed ya bukaci kotun da ta sa wata rana don cigaba da shari'ar tare da adana wadanda ake zargin a gidan gyaran hali.

Lauyan wadanda ake kara, Rabiu Sani, ya bukaci kotun da ta bayar da belin wadanda ake karar wanda Jastis Amina A. Aliyu ta amince.

Ya aminta da cewa, belin wadanda ake karar ya zaman N100,000 kowannensu tare da tsayayyu biyu.

Daya daga cikin tsayayyun ya kasance ma'aikaci a ma'aikatar sharia'a a mataki na 12 sai kuma daya shima ya kasance ma'aikaci a ma'aikatar shari'ar. Ta bukaci da a cigaba da tsare wadanda ake zargin har zuwa lokacin da za su cika sharuddan belin.

An dage sauraron kara zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel