'Yan sanda sun dakile harin da 'yan fashi suka kai bankin CBN

'Yan sanda sun dakile harin da 'yan fashi suka kai bankin CBN

Da yammacin ranar Talata ne rundunar 'yan sanda ta dakile yunkurin fashi da makami a babban bakin kasa (CBN) reshen Benin, jihar Edo.

'Yan fashin sun yi yunkurin kutsa wa cikin bankin a dadidai lokacin da babbar daukan kudi ke kokarin barin harabar bankin bayan an loda mata kudin da zata kai wani banki.

Amma, 'yan sandan da ke aiki a bankin sun dakile yunkurin 'yan fashin.

Musayar wutar da aka yi a tsakanin jami'an 'yan sandan da 'yan fashin ta sa jama'a ranta wa cikin na kare domin neman mafaka.

Wani shaidar gani da ido ya shaida wa manema labarai cewa duk da babu asarar rai sakamakon musayar wutar, amma harkokin kasuwanci a yanki da kewayen banki sun tsaya cak, masu shagunan sana'a sun hanzarta rufe wa.

Rundunar 'yan sanda ta kara yawan jami'an tsaro a bankin duk da a fatattaki 'yan fashin da suka kai harin sun tsere

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Mista Chidi Nwabuzor, bai samu ba saboda duk wayoyinsa na hannu a kashe suke lokacin da aka kira shi kafin wallafa wannan labari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel