Hotunan kayayyakin da gobara ta lallata a gidan gwamnatin Neja

Hotunan kayayyakin da gobara ta lallata a gidan gwamnatin Neja

Ofishin babban sakataren gwamnatin jihar Neja ya kama da wuta wacce ta fareu ne sanadin wutar lantarki.

Babban sakatariyar yada labarai ta gwamnan jihar Neja, Mrs. Mary Berje, ta ce an kai motocin kashe gobara na gidan gwamnatin jihar sabis kamar yadda aka saba lokacin da lamarin ya auku.

Ana gyaran ofishin ne yayin da gobarar ta barke da wajen karfe 2:30 na rana. An dau mintina 15 kafin masu kashe wuta na jihar su iso wajen don kashe gobarar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, an ga ma'aikatan gidan gwamnatin jihar na gudu don tseratar da rayukansu kafin masu kashe gobarar su iso da motoci uku na kashe gobara.

Hotunan kayayyakin da gobara ta lallata a gidan gwamnatin Neja

Hotunan kayayyakin da gobara ta lallata a gidan gwamnatin Neja
Source: Twitter

Gobara ta tashi a gidan gwamnatin jihar Neja (Hotuna)

Wasu kayayyki da aka ceto daga gobarar da ta tashi a gidan gwamnatin jihar Neja
Source: Twitter

Gobara ta tashi a gidan gwamnatin jihar Neja (Hoto)

Kujeru da wasu kayan daki da gobara ta lalata a gidan gwamnatin jihar Neja
Source: Twitter

Ofishin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa, kayayyakin ofishin, wasu abubuwa masu amfani da takardu masu muhimmanci sun kurmushe a gobarar. Kamfanin dillancin labaran Najeriya din ya gano cewa babu motocin kashe gobara na gidan gwamnatin jihar Nejan.

Mataimakin shugaban hukumar kashe gobara ta jihar, Mr Salihu Bello, wanda yayi magana da manema labarai a inda lamarin ya faru, yace hanzarin zuwan mutanensa wajen ne ya rage barnar da wuta tayi.

Ya ce rashin motocin kashe gobarar na gidan gwamnatin ba da gangan bane saboda ana ta shirye-shiryen kawo daya.

"Muna da ma'aikatanmu da suke amsa kira a duk lokacin da aka bukaci wani lamarin gaggawa," in ji shi.

Bello ya ce, motocin kashe gobarar da suka hallara a wajen sun zo ne daga sassa daban-daban na garin Minna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel