NDLEA ta cafke dan sanda da ake zargi da samar wa da 'yan Boko Haram miyagun kwayoyi

NDLEA ta cafke dan sanda da ake zargi da samar wa da 'yan Boko Haram miyagun kwayoyi

Hukumar yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi, NDLEA a jihar Yobe ta cafke wani dan sanda mai safarar miyagun kwayoyi da ake zargin yana hada kai tare da samarwa 'yan ta'addan Boko Haram haramtattun maganin Tramadol a Gwoza jihar Barno.

Reuben Apeh, shugaban hukumar NDLEA din ta jihar Yobe, ya tabbatar da kama wanda ake zargin a ranar 7 ga watan Nuwamba, yayin da yake zantawa da manema labarai.

Mr Apeh, yace mai safarar kwayoyin ya amsa laifinsa na saro miyagun kwayoyin daga wani jami'in hukumar kwastam a jihar Legas.

"Ya amsa samar wa da 'yan ta'addan miyagun kwayoyin inda ya ke kai musu Maiduguri kafin ya karasa musu dasu zuwa Gwoza. Ya yi ikirarin cewa, ya samo kwayoyin ne daga wani jami'in kwastam a jihar Legas kuma ya na siyar masa ne akan naira miliyan 6 a maimakon naira miliyan 24 da suke a kasuwa," in ji shugaban.

DUBA WANNAN: Kasar Saudiyya na yunkurin yin dokar hana aurar da mata 'yan kasa da shekaru 18

"Muna cigaba da bincikarsa don samun bayanai akan jami'in kwastam din da ya saro miyagun kwayoyin daga wajensa tare da wadanda suke taimaka masa har ya ke kawosu jihar. Ana kawo miyagun kwayoyin ne daga Legas zuwa Jos inda ake kaisu Maiduguri wajen dan sandan don isar dasu ga 'yan ta'addan," Apeh yace.

Yace, za a gurfanar da wadanda ake zargin gaban kuliya don karbar hukuncin da ya dace dasu.

Shugaban hukumar yayi kira ga sauran masu ruwa da tsaki da su hada kai da cibiyoyin tsaron don kawo karshen wannan barakar ta safara da ta'ammali da miyagun kwayoyi.

Apeh ya kara da jinjinawa jami'an hukumar sakamakon jajircewarsu da sadaukarwa ga aikinsu "kun yi abinda ya cancanci yabo kuma hukumar na tunkaho daku".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel