Babbar magana: APC ta dakatar da Oshiomhole

Babbar magana: APC ta dakatar da Oshiomhole

Jam'iyyarr APC reshen jihar Edo ta sanar da dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, bisa zarginsa da hannu a rikicin da APC ke fama dashi a jihar.

Jam'iyyar ta yanke shawarar dakatar da OShiomhole ne biyo bayan kada kuri'ar rashin amince wa da shi da shuwagabannin jam'iyyar APC a kananan hukumomi 18 a jihar Edo suka yi.

A cewar wani jawabin da shugaban jam'iyyar APC a jihar Edo, Anselm Ojezua, da mataimakin sakataren jam'iyyar, Ikuenobe Anthony suka fitar, sun bayyana cewa, "Shugabannin jam'iyyar sun zauna domin duba halin da APC ke ciki a jihar Edo, kuma sun nuna rashin amince wa da shi, lamarin da yasa suka kada kuri'a tare da amincewa da dakatar da shi daga jam'iyyar a matakin jiha."

DUBA WANNAN: Oshiomhole: Tsohon dan takarar gwamna a PDP ya koma APC a jihar Ed

Sun kara da cewa, daukar matakin ya zama dole ne domin kiyaye faruwar irin abinda ya faru a jihar Zamfara.inda APC ta shiga zabe ba tare da fidda 'yan takara ba.

"Adams Oshiomhole ne tushen duk rikicin da APC ke fama dashi a jihar Edo. Mun kada kuri'ar nuna rashin amincewar mu da shi.

"Bama son abinda ya faru a jihar Zamfara da sauran wasu sassan Najeriya ya maimaita kansa a jihar Edo," a cewar jawabin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel