Majalisa za ta amince da kasafin kudin Buhari a watan Nuwamba – Ahmad Lawan

Majalisa za ta amince da kasafin kudin Buhari a watan Nuwamba – Ahmad Lawan

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa majalisar ka iya kammala aikin tabbatar da kasafin kudin shekarar 2020 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika mata zuwa ranar 28 ga watan Nuwamba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban majalisar ya bukaci kwamitin kasafin kudi na majalisar ta gaggauta mika ma majalisa rahotonta zuwa ranar 26 ga watan Nuwamba domin cimma wannna manufa.

KU KARANTA: Yan majalsa sun tsige mataimakin kaakakin majalisar dokokin jahar Gombe

Mai magana da yawun Sanata Ahmad Lawan, Ezrel Tabiowo ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba, inda yace shugaban majalisar ya bada wannan umarni ne a zauren majalisar.

A cewar Sanatan, idan har kwamitin kasafin kudi ta majalisar ta mika rahotonta, yan majalisan za su iya amincewa da kasafin kudin zuwa ranar 28 ga watan Nuwamba kafin su tafi hutun kirismeti na karshen shekarar 2019.

“Dukkanin sauran kwamitocin sun kammala ayyukansu, kuma sun gudanar da ayyukan yadda ya kamata, a yanzu saura kwamitin kasafin kudi kawai muke jira, amma muna sa ran su kawo mana rahotonsu zuwa 26 ga watan Nuwamba, nan da makonni 2.

“Ina fatan ita ma majalisar wakilai haka za ta yi, domin su samu mu amince da kasafin kudin gaba dayanmu a ranar 28 ga watan Nuwamba, cikin ikon Allah.” Inji shi.

Sai dai kafin majalisar ta kammala zamanta, akwai wasu kudurori guda 12 da suka tsallake karatu na farko wadanda Sanatoci daban daban suka gabatar a gaban majalisar.

Daga cikin wadannan kudurori akwai: Kudurin samar da hukumar daidaito a addinai daga wajen Sanata Stella Oduah, kudurin kafa kwalejin yaki daga wajen Sanata Aliyu Wammako, kudurin kafa jami’ar noma da kimiyya a Funtua daga wajen Sanata Mandiya, kudurin kafa jami’ar gwamnatin tarayya a Gashau daga Sanata Yahaya Abdullahi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel