Yanzu Yanzu: IGP da Shugaban INEC sun sha barkonon tsohuwa a Lokoja

Yanzu Yanzu: IGP da Shugaban INEC sun sha barkonon tsohuwa a Lokoja

- Sufeto janar na yan sanda, Muhammed Adamu, Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, tare da kwamishinonin zabe na kasa sun sha barkonon tsohuwa a Lokoja

- Hakan ya faru ne lokacin da yan sanda ke kokarin kwantar da wani hargitsi a wajen taron kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin yan takarar a zaben gwamnan jihar Kogi mai zuwa

- Lamarin ya faru ne lokacin da wasu da ake zargin yan daban jam’iyya mai mulki ne, suka hana yar takarar gwamna na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Natasha Akpoti, shiga ajen taron ta karfin tuwo

Manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da Sufeto janar na yan sanda, Muhammed Adamu, Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, tare da kwamishinonin zabe na kasa, a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba sun sha barkonon tsohuwa yayinda yan sanda ke kokarin kwantar da wani hargitsi.

Saura kiris taron shiga yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin jam’iyyun siyasa da yan takararsu wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta shirya, tare da manyan jami’an yan sanda ya tarwatse lokacin da wasu da ake zargin yan daban jam’iyya mai mulki ne, suka hana yar takarar gwamna na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Natasha Akpoti, shiga ajen taron ta karfin tuwo.

Wajen ya kaure da hayaniya na kusan mintuna 20 a ainahin mashigin dakin taron, inda kungiyoyin biyu na masu kokarin shigar da yar takarar da masu yunkurin hana ta shiga suka dunga fafutukar samun shiga wajen.

Sai dai kuma a yayinda kungiyoyin biyu suka ki sauraron umurni daga jami’an tsaro, sai yan sanda suka harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa kungiyoyin daga mashigin.

KU KARANTA KUMA: APC ta ce karya ne PDP ba ta yi mata zigidir ba a Zamfara

Radadin barkonon tsohuwar ya shiga har cikin dakin taron, inda akan ya samu dukkanin mutanen da ke ciki, harda IGP, wanda aka gano ya toshe hancinsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel