Oshiomhole: Tsohon dan takarar gwamna a PDP ya koma APC a jihar Edo

Oshiomhole: Tsohon dan takarar gwamna a PDP ya koma APC a jihar Edo

Akwai yuwuwar tsohon sakataren gwamnatin jihar Edo, Fasto Osagie Ize-Iyamu zai koma jam'iyyar APC daga jam'iyyar PDP.

Ize-Iyamu, dan takarar kujerar jihar gwamnan Edo ne a zaben 2015 karkashin jam'iyyar PDP. Ya tabbatar da hakan ne a tattaunawar waya da suka yi da wakilin jaridar Tribune Online a jiya. Yace, ya yanke hukuncin barin jam;iyyar PDP ne sakamakon kiransa da magoya bayansa ke yi akan ya "dawo gida".

Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC din na yankin kudu-kudun yana Abuja a halin yanzu don kammala canza shekar.

DUBA WANNAN: Ministocin Buhari 22 da babu su a shafin yanar gizo na gwamnatin tarayya

Yace yunkurin sasanta bangarorin jam'iyyar PDP din da ke fada da yayi duk ya tashi a tutar babu. Hakan yana daga cikin dalilan da yasa ya bar jam'iyyar don komawa APC.

Ya ce yana Abuja ne don kammala shirye-shiryen komawa jam'iyyar APC wanda za a yi shagalin bidirin a babban birnin jihar Edo.

Ize-Iyamu ya jaddada cewa, a matsayinsa na jigo a kafa jam'iyyar AC wacce ta koma ACN daga baya ta koma APC, kawai zai koma gida ne ba wai canza sheka ba.

Ya ce: "Da gaske ne zan bar jam'iyyar PDP don komawa APC. Bana ji a jikina canza sheka zanyi, komawa gida zanyi. Zan bar PDP ne saboda matsalolin da suka yi kaka-gida a jam'iyyar wadanda nayi kokarin sasantawa amma ba nasara. Ba jita-jita bane, zan koam gida ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel