Rufe iyakokin Najeriya: Zamu karyar da farashin shinkafa - Santus

Rufe iyakokin Najeriya: Zamu karyar da farashin shinkafa - Santus

Shugaban wani kamfanin sarrafa kayan abinci, da ke samar da wata shinkafa, ya ce sun kammala duk wani shiri domin zabtare farashin buhun shinkafa zuwa N14,000 kafin lokacin bikin Kirsimeti da sabuwar shekara.

Cif Paul Santus, shugaban kamfanin sarrafa kayan abinci da suka hada da shinkafar 'Ojota', ya bayyana cewa kamfaninsa ya kammala dukkan wani shiri domin mayar da farashin buhun shinkafar 'Ojota' mai nauyin kilogram 50 (50Kg) zuwa N14,500 domin 'yan Najeriya su samu sukunin yin shagulgulan bikin Kirsimeti da sabuwar shekara a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ta rufe iyakokinta na kasa da makwabtan kasashe.

Santus ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin wata hira da jaridar Vanguard a kan irin kalubalen da ke kan kamfaninsa sakamakon rufe iyakokin kasa da kuma yin karin bayani a kan dalilin da yasa kamfaninsa ya rubanya adadin shinkafar da yake samar wa a matsuguninsa da ke O'akwa-Okpoma a karamar hukumar Yala, jihar Kuros Riba.

Ya ce kar 'yan Najeriya su samu damuwa a kan yiwuwar samun tashin farashin shinkafa a yayin da ake tunkarar lokacin bukukuwa domin kamfaninsa ya kammala shirin dakile tashin gwauron zabin da farashin shinkafar kan iya yi sakamakon rufe iyakokin kasa da gwamnati ta yi

DUBA WANNAN: An kai hari gidan casun Saudiyya

Farashin shinkafa ya ya yi tashin gwauron zabi har zuwa N22,00 sakamakon rufe iyakokin Najeriya da gwamnatin tarayya ta yi.

"Mu a kamfanin 'Santuscom Agro-hub Investment Limited', masu sarrafa shinkafar 'Ogoja Rice' mun damu da batun tashin gwauron zabin da farashin shinkafa ya yi sakamakon rufe iyakokin kasa da gwamnati ta yi.

"Mu na so 'yan Najeriya su fahimci dalilan gwamnati na rufe iyakokin, sannan muna yi wa jama'a albishir din cewa kamfaninmu ya kammala duk wani shiri domin sayar da buhun shinkafa ga 'yan Najeriya a kan farashin N14,000 kafin lokacin bikin Kirsimeti da sabuwar shekara," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel