Da duminsa: Kotu ta haramtawa dan takarar mataimakin gwamnan APC takara

Da duminsa: Kotu ta haramtawa dan takarar mataimakin gwamnan APC takara

Babban kotun tarayya dake zamanta a Abuja ranar Talata ta haramtawa, Biobarakuma Degi, takarar kujeran mataimakin gwamnan jihar Bayelsa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC.

Kotun ta yanke hukuncin ana saura kwanaki shida zabe.

Justice Inyang Ekwo ya yanke hukuncin ne kan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1101/2019 da jam'iyyar Peoples Democratic Party ta shigar.

Za'a gudanar da zaben jihar Bayelsa ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2019.

KARANTA Hukumar Sojin ruwa ta karawa manyan jami'anta 140 matsayi (Jerin sunayensu)

A bangare guda, Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, tayi zargin cewa gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, da jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, sun sayi rigunan yan sanda da Soji na bogi.

Hakazalika an yi zargin cewa PDP ta kera katunan zabe na bogi domin kawo rikici zabe ranar 16 ga Nuwamba, 2019.

A wani jawabin da mataimakin kakakin APC, Yekini Nabena, ya tuhumci gwamna Seriake Dickson, da sakin wasu fursunoni 100 daga gidan yarin Okaka domin amfani da su lokacin zabe.

A cewarsa, gwamnatin jihar na shirin baiwa mutane dubu ashirin-ashirin a ranar zabe domin su zabi jam'iyyar PDP.

Mataimakin Kakakin APC na kasa ya ce banda binciken leken asirin da suka samu, wasu yan cikin gidan gwamnan sun bayyana yadda PDP ke shirin tafka magudi a ranar Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel