Assha: Masu garkuwa da mutane sun kashe wani dan kasuwa bayan sun karbi kudin fansa a jihar Nasarawa

Assha: Masu garkuwa da mutane sun kashe wani dan kasuwa bayan sun karbi kudin fansa a jihar Nasarawa

Masu gakuwa da mutane sun kashe wani dan kasuwa mai suna Osondu Nwachukwu da suka sace duk da cewa sun karbi kudin fansa domin sakinsa a jiha Nasarawa.

A wata hira da aka yi da su, iyalan Nwachukwu sun yi kira gwamnatin da ta sake dauka mataki kan kalubalen da tsaron kasar ke ciki a matakan jiha da na tarayya.

Nwachukwu mai shekara 55 a duniya, a zama a Nasarawa sama da shekaru 30 da suka gabata sannan ya kasance yana sana’ar ruwan leda inda yake amfani da gidansa wajen gudanar da wannan harka.

Fasto dinsa, Reverend Father Joshua Obile, ya bayyana shi a matsayin mutum mai son zaman lafiya wanda babban burinsa shine daukar dawainiyar iyalinsa.

Babban malamin na Kirista ya ce: “Baya son fitina da kowa, da wuya ka ga yana musayar yawu da mutane.

“Mutum ne mai son zaman lafiya, harma a gidansa a duk lokacin da na kai ziyara, za ka ganshi yana gudanar da harkoki da kansa. Ya kasance mutum mai jajircewa da biyayya.”

A ranar 30 ga watan Oktoba ne yan fashi suka sace Nwachukwu daga gidansa bayan sun sace masa kudade, takardun gidansa da wasu muhimman abubuwa.

KU KARANTA KUMA: Dankari: Sabon rikici ya kunno kai a PDP Edo yayinda aka dakatar da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar

Bayan yan kwanaki a hannunsu, sai suka bukaci a biya naia miliyan 20 a matsayin kudin fansarsa, inda bayan an sha rokonsu sai suka rage zuwa miliyan 10 sannan suka koma N40,000 wanda aka biya. Sai dai kuma, bai dawo da ransa ba.

A wani labarin kuma mun ji cewa wani matashi dan shekara 28 Babatunde Damilare ya kashe wata mata dake harkar karuwanci a jahar Legas sakamakon takaddama data barke a tsakaninsu kan kudin ta da ya kekashe kasa ya ki biyanta, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyarmu ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a daren Juma’a, 8 ga watan Nuwamba a wani gidan karuwai dake layin Atan, cikin unguwar Surulere na jahar Legas inda matashin ya tafi don yin zina da wata karuwa mai suna Elochukuwu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel