Yanzu Yanzu: APC reshen Edo ta tsige Lawrence Okah daga matsayin sakatarenta

Yanzu Yanzu: APC reshen Edo ta tsige Lawrence Okah daga matsayin sakatarenta

- Jam’iyyar APC reshen jihar Edo ta tsige Mista Lawrence Okah daga matsayin babban sakatarenta a jihar

- An yanke hukuncin ne bayan wata ganawa da kwamitin zartarwa na jihar suka yi a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba, inda aka gabatar da kuri’un rashin gamsuwa akan Okah

- Sun kuma jaddada goyon bayansu ga shugaban jam'iyyar a jihar, Barista Anselm Ojezua

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Edo ta tsige babban sakataren jam’iyyar a jihar, Mista Lawrence Okah.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi dauke da sa hannun mataimakin sakataren jihar, Mista Ikuenobe Anthony.

Jawabin ya bayyana cewa an yanke hukuncin ne bayan wata ganawa da kwamitin zartarwa na jihar suka yi a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba, inda aka gabatar da kuri’un rashin gamsuwa akan Okah.

A cewarsa: “Kwamitin zartarwa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar a safiya yau, 12 ga watan Nuwamba, 2019, sun gabatar da kuri’un rashin gamsuwa akan sakataren jam’iyyar na jihar, Mista Lawrence Okah, kamar yyadda yake a kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

"Hakan na nufiun cewa daga yanzu Mista Lawence Okah ya tashi daga sakataen jam'iyyar a jihar.

"Za a maye gubinsa da wanda ya dace a lokacin da ya kamata kamar yadda yake a sashi na 17 (vi) na kundin tsarin mulkin jam'iyyar."

Jawabin ya kara da cewa an isar da kuri'ar yarda a kan shugaban jam'iyyar a jihar, Barista Anselm Ojezua.

KU KARANTA KUMA: Zabukan Bayelsa da Kogi: Tsohon gwamna Dankwambo ya gargadi APC

A wani labari na daban, mun ji cewa ana saura kwanaki shida zaben gwamnan jihar Bayelsa, kakakin majalisar dokokin jihar, Rt Hon Monday Obolo Bobou, da magoya bayansa sun sauya sheka daga jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) zuwa All Progressive Congress (APC).

Hakazalika shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Southern Ijaw, Hanarabul Nigeria Kia, ya sheke APC.

Dukkan wadanda suka koma APC yan karamar hukumar Southern Ijaw ne, mahaifar dan takaran jam'iyyar APC, David Lyon.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel