Hukunci ko azaba: Wani ya kulle kanwarsa a daki na tsawon shekara biyu a jihar Kaduna

Hukunci ko azaba: Wani ya kulle kanwarsa a daki na tsawon shekara biyu a jihar Kaduna

- A jiya Litinin ne wata kungiyar tallafin mata da ke Kaduna ta ceto wata baiwar Allah daga bakin kangin da ta fada

- Yarinyar mai suna Hassana Yayanta ya garkameta a daki ne na tsawon shekaru biyu saboda zata koma gidan mijinta kuma uban 'ya'yanta guda hudu

- Dakin wanda ko siminti babu balle tabarma ya koma sabuwar duniya ga Hassana don kuwa a nan take fitsari, kashi, bacci da cin abinci

Hajiya Rabi Salisu, shugabar kungiyar Arrida Relief Foundation da ke Kaduna, ta gano wata baiwar Allah da yayanta ya kulleta na tsawon shekaru biyu a daki a unguwar Rigasa dake jihar Kaduna.

A yunkurin tallafawa mata da Hajiya Rabi Salisu ke yi, ta bankado wata mata mai suna Hassana dake yankin unguwar Rigasa a cikin jihar Kaduna.

Dalilin da yasa yayanta yin hakan kuwa shine, Hassana dai ta dage sai ta koma gidan mijinta, uban 'ya'yanta guda hudu wanda suka rabu da farko. Danginta sun zargi mijin Hassana da jefata cikin damuwa inda daga bisani ya saketa.

KU KARANTA: Cikin daren jiya ina ji ina gani makwabcina yayi mini fyade wallahi kashe kaina zanyi - Budurwa ta sha alwashi

Don haka ne yayanata ya yanke hukuncin kulleta a cikin daki wanda babu ko siminti cikinsa. Dakin mai cike da yashi babu ko tabarma shine ya kasance mazaunin Hassana na shekaru biyu. A nan take bayan gida fitsari, bacci da cin abinci.

A jiya, Litinin 11 ga watan Nuwambar shekarar 2019, Arrida Relief Foundation ta ceto Hassana daga kangin da ta fada na shekaru biyu. A hakan ne kuma suka garzaya da ita asibiti don duba lafiyarta.

Kungiyar tana kira ga hukumomi da kuma kungiyoyi da su shigo lamarin don kwatarwa Hassana hakkinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel