Kasar Saudiyya na yunkurin yin dokar hana aurar da mata 'yan kasa da shekaru 18

Kasar Saudiyya na yunkurin yin dokar hana aurar da mata 'yan kasa da shekaru 18

- Hukumar kare hakkin dan adam ta Saudiyya ta bada shawarar kafa dokar haramtawa 'yan matan da basu kai shekaru 18 aure a kasar

- Kamar yadda hukumar ta ce, duk yarinyar da bata kai shekaru 18 ba toh bata mallaki hankali ba

- Sanarwar ta bayyana cewa yi wa kananan yara aure na da illoli ga tunaninsu da kuma lafiyarsu

Hukumar kare hakkin bil adama ta kasar Saudiyya ta bada shawarar kafa dokar haramtawa 'yan matan da ba su kai shekaru 18 aure a kasar.

Jaridar yanar gizo ta Saudi Gazette, ta ruwaito cewa, hukumar ta bayyana cewa, duk yarinyar da bata kai shekaru 18 a duniya ba, toh tabbas bata mallaki hankali ba kuma bata isa aure ba.

Sanarwar ta bayyana cewa, aurar da yarinyar da bata kai shekaru 18 ba a kasar ta yi karantsaye ga dokokin kasar masu yin kariya ga kananan yara da hana ci musu zarafi tare da safararsu.

DUBA WANNAN: Wasu abubuwa 5 da jama'a basu sani ba a kan Mamman Daura

Hukumar kare 'yancin dan adam din ta Saudiyya ta ce "Dokar farko ta dokokin kare 'yancin kananan yara na duniya wadanda masarautar kasar take bi sau da kafa, sun ce duk wanda bai kai shekaru 18 a kasar ba toh tabbas yaro ne ko yarinya."

Hukumar ta cigaba da bayyana illolin da ake haduwa dasu sakamakon aurar da kananan yara, inda tace nazarin da tayi, tayi shi ne da wasu kungiyoyi.

Ta ce "Illar auren wuri ga yara yana hadawa da tunaninsu da yanayin jikinsu."

Tabbatar da dokar hana yi wa kananan yaran aure zai bada kariya garesu da lafiyar jikinsu. Hakan kuma zai bunkasa zaman lafiya tsakanin ma'aurata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel