Dankari: Sabon rikici ya kunno kai a PDP Edo yayinda aka dakatar da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar

Dankari: Sabon rikici ya kunno kai a PDP Edo yayinda aka dakatar da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar

Rikicin cikin gida ya kunno kai a Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Edo, yayinda wata fegi na jam’iyyar ta sanar da dakata da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar a fadin yankuna uku da ke jihar.

Wadanda aka dakatar sun hada da tsohon ministan harkokin waje, Cif Tom Ikimi, tsohon Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa, Cif Mike Oghiadohme, tsohon ministan ayyuka, Arch.Mike Onolememen, Cif Raymond Dokpesi, Sanata Yisa Braimoh, Sanata Victor Oyofo da kuma wani tsohon Shugaban majalisar wakilai, Tunde Akogun.

Dakatarwar nasu na kunshe ne a cikin wata takardar yarjejeniya dauke da sa hannun tsohon Shugaban kungiyar kwallon kafa na Najeriya, Emperor Jarret Tenebe da tsohon Shugaban karamar hukumar Owan ta yamma, Dan Asekhema bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a karshen makon da ya gabata a Benin.

A takardar yarjejeniyar, sun nuna karfin gwiwa a kan Shugaban jam’iyyar na jihar, Cif Dan Obih sannan suka bashi karin watanni shida domin basu damar gudanar da zaben fidda gwani na gwamna.

Da yake bayani kan dalilin dakatar da wasu daga cikin shugabannin, takardar ya yi bayanin cewa “An gano Cif Oghiadohme a lokacin da ya shiga jirgi mai saukar ungulu tare da gwamna Godwin Obaseki a karshen makon da ya gabata domin halartan bikin yaye dalibai a jami’ar Edo Iyamho.

“Harma ya nuna alamar 4+4, wanda ke lamuncewa tazarcen Obaseki alhalin muna da dan takaarmu na PDP. Cif Ikime da sauransu sun yi ta ganawa da Gwamna Obaseki inda muka samu bayanin cewa an bukaci gwamnan ya kawo naira biliyan shiuda domin ya samu komawa PDP sannan ya mallaki tikitin takara."

KU KARANTA KUMA: Zabukan Bayelsa da Kogi: Tsohon gwamna Dankwambo ya gargadi APC

Sai dai kuma Cif Orbih wanda ya yi watsi da Karin watanni shida da aka yi masa ya ce baida masaniya a kan kowace kungiya mai suna PDP integrity group.

Ya bukaci jama’a da su yi watsi da duk wani jawabi da kungiyar ta saki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Online view pixel