Yanzu-yanzu: Ana saura kwana 6 zabe, Kakakin majalisa, shugaban jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC a Bayelsa

Yanzu-yanzu: Ana saura kwana 6 zabe, Kakakin majalisa, shugaban jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC a Bayelsa

Ana saura kwanaki shida zaben gwamnan jihar Bayelsa, kakakin majalisar dokokin jihar, Rt Hon Monday Obolo Bobou, da magoya bayansa sun sauya sheka daga jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) zuwa All Progressive Congress (APC).

Hakazalika shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Southern Ijaw, Hanarabul Nigeria Kia, ya sheke APC.

Dukkan wadanda suka koma APC yan karamar hukumar Southern Ijaw ne, mahaifar dan takaran jam'iyyar APC, David Lyon.

Tsohon hadimin gwamnan Bayelsa, Tony Oki, wanda shi ma ya sauya sheka ya ce sun yanke shawaran fita daga PDP ne saboda yan jihar Bayelsa sun gaji da gwamnatin PDP kuma dan takarar APC yafi su manufa mai kyau ga jihar.

Yayinda yake tarban sabbin yan jam'iyyar wurare daban-daban a karamar hukumar, dan takarar gwamnan, David Lyon, ya ce APC zata lallasa PDP a zabe domin gyara lalatan PDP ta rika yi tun shekarar 2012.

A wani labarin daban, Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, tayi zargin cewa gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, da jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, sun sayi rigunan yan sanda da Soji na bogi.

Hakazalika an yi zargin cewa PDP ta kera katunan zabe na bogi domin kawo rikici zabe ranar 16 ga Nuwamba, 2019.

A wani jawabin da mataimakin kakakin APC, Yekini Nabena, ya tuhumci gwamna Seriake Dickson, da sakin wasu fursunoni 100 daga gidan yarin Okaka domin amfani da su lokacin zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel