Kungiya ta bukaci Shugaba Buhari ya dawo da Hadiman Mataimakin Shugaban kasa

Kungiya ta bukaci Shugaba Buhari ya dawo da Hadiman Mataimakin Shugaban kasa

Bayan tsige wasu daga cikin Hadiman fadar shugaban kasa, kungiyar Nigerian Youths Alliance ta Matasan Najeriya, ta fito ta na rokon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake duba lamarin.

Shugaban Kungiyar ta Nigerian Youths Alliance ta na so shugaban kasa Buhari ya yi hakuri ya maida wadannan Masu bada shawara a ofishin mataimakin shugaban kasar zuwa bakin aikinsu.

Akinsiji Ololade ya yi wannan jawabi ne a Ranar Litinin, 11 ga Watan Nuwamban 2019 a Garin Akure da ke jihar Ondo. Ololade ya ce Yarbawa aka hara da tsige Hadiman fadar shugaban kasar.

Mista Akinsiji Ololade ya ke cewa mafi yawan wadanda wannan sallama daga aikin ya shafa, Mutasan Yarbawa ne. Ololade ya kuma yi kira ga sauran kungiyoyin Matasa su tashi su yi bore.

Kungiyar Matasan ta na so sauran Takwarorinta a fadin kasar su nuna rashin jin dadinsu game da matakin da gwamnatin shugaba Buhari ta dauka na fatattakar wadanda su ka yi masa yaki.

KU KARANTA: Hadimin Shugaban kasa ya yi magana a kan korar da aka yi

“A matsayinmu na kungiya, mun san cewa shugaban kasa ya na da damar dauka da sallamar aiki, amma an zazzage duk Matasan da shugaban kasar ya taba godewa kokarinsu wajen kafa mulki.”

Kungiyar ta ji takaicin wannan abu inda ta ce: “La’akari da cewa babu wani laifi da aka samu Hadiman da shi, za a iya cewa Buhari ba zai iya boye kiyayyarsa na ganin Matasa a mulki ba ne.”

Matashin ya ke cewa duk da Muhammadu Buhari ya fara samun mulki ne a lokacin ya na da shekaru 40, yanzu bai sha’awar ganin Matasa sun taso ana damawa da su a cikin gwamnati.

Shugaban kungiyar Matasan ya yi kira ga shugaban kasar ya ba Matasa dama a gwamnatinsa inda ya tuna masa cewa mafi yawan kasashen da su ka cigaba, su na aiki ne da Matasansu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel