Zabukan Bayelsa da Kogi: Tsohon gwamna Dankwambo ya gargadi APC

Zabukan Bayelsa da Kogi: Tsohon gwamna Dankwambo ya gargadi APC

- Ibrahim Dankwambo ya gargadi APC a kan zabukan Kogi da Bayelsa masu zuwa

- Tsohon gwamnan ya ce APC na so mutanen Kogi su zabi dan takarar da bai tabuka wani abun kirki ba yayinda suke neman yan Bayelsa su yi waje da jam’iyya mai kokari

- A cewar Dankwambo, babu wani alama na gwamnati a Kogi a shekaru hudu da suka gabata

Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo ya gargadi All Progress (APC) a kan matsayarsu game da zabukan jihohin Kogi da Bayelsa masu zuwa.

Jigon na jam’iyyar PDP a shafinsa na Facebook ya soki jam’yya mai mulki kan kira da ta yi ga mutanen jihohi masu mutunci akan su zabi yan takararsu duk da cewar yan takarar PDP sun yi kokari fiye da nasu yan takarar.

A cewar Dankwambo, daya daga cikin irin wadannan gwamna na rike da albashin ma’aikata na sama da watanni 30 duk da kudin tallafi sannan duk da wannan, jam’iyyar na neman mutaen jihar su zabe shi yayinda suke neman mutane a Bayelsa da kada su zabi PDP wacce gwamnanta ya yi bajinta sama da na APC.

Game da jihar Kogi, tsohon gwamnan ya kaddamar da cewa babu wani alamu da ke nuna akwai gwamnati a jihar a shekau hudu da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: Na dauki kasada na nemawa mutum 157, 000 aiki a Jihar Edo – Gwamna Obaseki

Musamman, ya ce babu wani aiki da aka yi duk da biliyoyin kudin da gwamnatin tarayya ta tura ma jihar.

A wani lamari na daban, mun ji cewa jam’iyyar adawa ta NCP ta na zargin APC mai mulki a jihar Katsina da bada makudan daloli domin sayen Alkalai a shari’ar karar zaben gwamnan jihar da aka yi.

NCP ta ce gwamnatin jihar Katsina ta bada cin hanci ne ga wani daga cikin Alkalan da su ka saurari korafin zaben 2019 a kotun karar zabe.

Gwamnati ta karyata wannan zargi mai nauyi. Darektan yada labarai na gwamna Aminu Masari watau Malam Abdu Labaran Malumfashi, ya yi watsi da wannan zargi inda ya ce babu wata hujja da za ta iya gamsar da jama’a a kan hakan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel