NCP, Gwamnatin Katsina, su na cacar baki kan zargin ‘sayen shari’a’ a Kotu

NCP, Gwamnatin Katsina, su na cacar baki kan zargin ‘sayen shari’a’ a Kotu

Mun samu labari dazu cewa jam’iyyar adawa ta NCP ta na zargin APC mai mulki a jihar Katsina da bada makudan daloli domin sayen Alkalai a shari’ar karar zaben gwamnan jihar da aka yi.

NCP ta ce gwamnatin jihar Katsina ta bada cin hanci ne ga wani daga cikin Alkalan da su ka saurari korafin zaben 2019 a kotun karar zabe. Gwamnati ta karyata wannan zargi mai nauyi.

Darektan yada labarai na gwamna Aminu Masari watau Malam Abdu Labaran Malumfashi, ya yi watsi da wannan zargi inda ya ce babu wata hujja da za ta iya gamsar da jama’a a kan hakan.

Da aka tuntubi Abdu Labaran Malumfashi, ya fadawa Manema labarai cewa: “Karya ce; ya tafi kotu idan ya tabbatar da hujjojinsa. Me zai hana shi tafiya wajen ICPC ko kuma EFCC, ko ma ina ne.”

Malumfashi ya ke cewa "Mai ya ke jira?" Inda ya ce duk mai zargin gwamnan da bada cin hanci da rashawa a kotu, ya kai kara. Sai dai ‘yan hamayyar sun ce ba da gaske ake yakar barna ba.

KU KARANTA: Manyan Gwamnonin PDP sun fara fada a kan takarar 2023

A wajen wani taro da jam’iyyar NCP ta kira, ta zargi APC da sayen shari’ar da kotu ta yi a zaben jihar Katsina ta hanyar bada rashawa ga Alkalai. Jam’iyyar hamayyar ta ce ta na da hujjojin ta.

Shugaban NPC na jihar Katsina gaba daya, Abdulmumin Sani, ya ke cewa: “Jam’iyyar APC ta na yaudarar mutane cewa ta na yaki da rashin gaskiya a jihohi da kuma gwamnatin tarayya…

…Amma yanzu kowa ya ga yadda APC ta ke tafka cin hanci da rashawa maimakon ta yake su a Katsina. Sabon misalin rashin gaskiyar APC a karkashin gwamnatin APC shi ne sayen shari’a.”

“Ta tabbata Aminu Bello Masari da APC a jihar Katsina sun bada kudi $193,700 ga daya daga cikin Alkalai uku da su ka saurari korafin zaben gwamna inda aka kalubalanci nasarar Gwamnan.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel