Na dauki kasada na nemawa mutum 157, 000 aiki a Jihar Edo – Gwamna Obaseki

Na dauki kasada na nemawa mutum 157, 000 aiki a Jihar Edo – Gwamna Obaseki

A Ranar Litinin, 10 ga Watan Nuwamban 2019, Mai girma gwamnan jihar Edo, Mista Godwin Obaseki, ya bayyana yadda ya yi wani gangancin da ya yi sanadiyyar samawa jama’ansa aikin yi.

Gwamnan ya bayyana cewa a cikin shekaru uku da su ka gabata, an samu mutane 157, 000 da su ka samu aikin yi a jihar Edo. Gwamnan ya ce ya yi wannan ne duk da shakkun da wasu su ka yi.

Godwin Obaseki ya bayyana wannan ne a wajen wani taron Matasa da aka shirya da ake kira ‘Alaghodaro’. Mista Obaseki ya ce ya kirkiro ayyukan yi ne ta dabarun da ya dauka a jihar Edo.

Daga cikin hanyoyin da gwamnan ya bi wajen ba Matasa aikin yi akwai sanarwa da bada horo a aikin hannu da kasuwanci, da kuma bin duk inda za a samu kwararru da su ka cancanci ayyukan.

Obaseki da ya ke jawabi wajen wannan taro da aka yi a Ranar 11 ga Wata, ya ce ya maida hankali ne a bangarori shida wadanda su ka hada da mutane harkar ilmi, bangaren wasanni da al’adu.

KU KARANTA: Ana juya kan Almajirai ana yin ta’adi da su a Najeriya - Malami

A wajen wannan taro, an horas da wasu Matasa 150 a bangaren fasaha. Matasa sama da 2000 ne su ka amfana a gaba daya wannan tsari da aka shirya, yanzu haka wasu kamfanoni na nemansu.

A bangaren ilmi, gwamnan ya ce a shekara mai zuwa zai kafa makarantu 300 inda za a rika koyar da aikin hannu. Gwamnan ya ce wannan zai sa duk wanda ya yi karatu ya iya neman abinci.

“Mu na so mu canza tunanin mutane cewa ilmi ba takardar shaida ba ce kawai. Shiyasa mu ka kawo ayyuka a Edo domin Matasa su samu abin yi. Mu na hangen shekaru 30 ne masu zuwa.”

Gwamnan Kudancin Najeriyar mai neman tazarce ya kuma bayyana cewa an kusa kammala aikin lantarkin jihar wanda zai bada dama a saki wuta a kan hanyoyin da ke cikin gari cikin dare.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel