Cikin daren jiya ina ji ina gani makwabcina yayi mini fyade wallahi kashe kaina zanyi - Budurwa ta sha alwashi

Cikin daren jiya ina ji ina gani makwabcina yayi mini fyade wallahi kashe kaina zanyi - Budurwa ta sha alwashi

- Wata matashiyar budurwa ta bayyana yadda wani makwabcinta yayi mata fyade

- Budurwar ta bayyanawa 'yan sanda cewa, ta bukaci ya rakata kofar gida ne saboda tsaro amma ya kare da keta mata haddi

- Ta ba 'yammata shawara da su dinga yawo da turaren barkonon tsohuwa gudun fadawa irin halin da ta shiga dalilin wannan makwabci na ta

Wata 'yar kasar Afirka ta kudu mai amfani da kafar sada zumunta ta Twitter, ta zargi makwabcinta da yi mata fyade bayan ta bukaci ya rakata gida saboda tsoro da take ji.

Matashiyar budurwar ta bayyana cewa mutumin yayi mata fyaden ne a ranar Asabar da yamma. Ta kai kara ga jami'an tsaro a ranar Lahadi da safe.

Ana zargin cewa wanda yayi mata fyaden ya tsere bayan da jami'an 'yan sanda suka bata lokaci kafin su je gidansa su kama shi.

KU KARANTA: Allahu Akbar: Anyi rabon gadon dukiyar marigayi Rabilu Musa Ibro

"Makwabcina yayi min fyade a daren jiya... Ji nake kamar in kashe kaina yanzu. Daga na nemi ya raka ni zuwa gida saboda tsoro da nake ji kuma na nuna na yarda da shi, lokacin da muka isa kofar gida sai labari ya canza, ban aune ba kawai sai ganin kaina nayi a kasa."

"Gaskiya ban taba tsammanin hakan zata faru dani ba ballantana kuma daga wanda na yarda da shi, shawara gareku mata, ku dinga yawo da turaren barkonon tsohuwa don kuwa karnukan nan na iya kawo hari a koda yaushe," Budurwar ta wallafa haka a shafinta na tuwita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel