Ana zaman dar-dar tsakanin Gwamnonin PDP saboda zaben 2023

Ana zaman dar-dar tsakanin Gwamnonin PDP saboda zaben 2023

Jaridar New Telegraph ta kawo kishin-kishin din cewa akwai baraka a tafiyar jam’iyyar PDP. Jaridar ta ce an samu rabuwar kai a cikin kungiyar gwamnonin babbar jam’iyyar hamayyar kasar.

A cewar rahoton, harin takara a zabe mai zuwa na 2023 ne ya fara gwara kan gwamnonin na jam’iyyar PDP. Hakan na zuwa ne bayan jam’iyyar ta karyata irin wannan rade-radi kwanakin baya.

Sababbin bayanan da su ke shigowa shi ne gwamnonin PDP sun rabu gida biyu; Da bangaren Nyesom Wike da kuma wasu manyan gwamnonin jam’iyyar da su ka zarce a kan mulki a zaben 2023.

Wadannan bangarori su na fada ne kan burin siyasarsu ta yadda kowa ke kokarin ganin jam’iyya ta zama hannunsa. Duk da bayanin Kola Ologbondiyan na kwanaki, majiyar ta cerikicin ya yi kamari.

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, zai gama mulki ne a 2023, haka zalika wadannan gwamnoni tara da ke kokarin taka masa burki. Ana zargin Wike ya na son su tsaya takara ne da Aminu Tambuwal.

KU KARANTA: PDP: APC ta na shirin canza Alkalan shari’ar zaben Jihar Kano

Tambuwal na jihar Sokoto ne ya zo na biyu a zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP. Gwamnan na Ribas shi ne ya tsaya tsayin-daka ya mara masa baya, amma tikitin ya fada hannun Atiku Abubakar.

Gwamnonin na PDP su na yunkurin ganin bayan wannan shiri da Nyesom Wike ya ke da shi har gobe na ganin ya tsaya takarar mataimakin shugaban kasa tare da gwamnan Sokoton a PDP a zaben 2023.

Wadannan gwamnoni da za su ja daga da Wike sun hada da na Benuwai, da jihar Taraba a Arewa. Sauran gwamnonin sun hada da na Ebonyi, Akwa Ibom, Abia, Kuros Riba, Enugu da kuma na jihar Delta.

Majiyar ta bayyana cewa: “Tabbas Wike ne ya kawo shugaban PDP na kasa, Prince Uche Secondus, domin ka gane wanda ke da iko a PDP. Amma ya ce gwamnonin da su ka dawo, ba su tare da shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel